AHLIL-BAITY JIRGIN TSIRA BABU MASU ILIMI DAGA KAKANKU {S} SAIKU {A.S} KU KARANTA KUJI

-Imam sadik (as) yace; “Da Mumini zai je ya hau tsororuwar dutse ya zauna (wato saboda gujewa matsalar mutane) da Allah (T) ya sallado masa wanda zai cutar da shi”.
                                                                          
-Manzon Allah (S) Yace; “Bai kasance a da ba, ko a Yanzu, ko nan gaba, har zuwa tashin kiyama, ga Annabi ko Mumini, face an samu wani Dan uwan sa na jini da ya ke cutar da shi”.

-Imam Ali (as) Yace: Manzon Allah (S) yace; “Da a ce Mumini zai shiga wani rami (wato saboda gujewa cutarwar Mutane) da Allah ta'ala Ya sallado Masa Wanda zai cutar da shi”.

-Imam Bakir (as) Yace; “Fari ya Samu Mutanen Annabi Hudu (as), sai suka tafi wajen sa domin yayi addu’ar Allah (T) ya saukar da ruwa. Suka je gidansa basu same shi ba, sai Matarsa ta fito, kawai sai ta fara yi Musu fada da hayaniya. Sai Suka ce mata, ‘to yana
ina?’ tace, ya tafi gona.

Sai suka samu Annabi Hudu (AS) a gona.
Da suka isa sai suka ga duk idan ya yi kunya guda daya na Shuka sai ya yi nafila raka’a biyu, Sai ya juya ya dubi mutanen yace, ‘menene bukatar ku?’ su kace; ‘Munzo wajen ka ne domin wata bukata’ , sai mu kaga abin da ya bamu mamaki’ sai ya tambaye su, me ya baku mamaki?

Sai Suka ce; ‘Mun ga wata mata ta fito daga gidan ka, tana mana fada da haniya’. Sai Annabi hudu (as) Yace masu; ‘Ai Matata ce, kuma duk da Wadannan Dabi’u nata, ina son cigaba da zama da ita’ Sai yace masu, babu wani Mumini face an samu wani da yake cutar da shi sai yace musu Ni ina godiya ga Allah ta'ala da ya sanya mai cutar da ni, yana karkashin iko na ne, ba domin haka ba da Allah ta'ala ya sallado min da Wanda ya fita cutarwa”.

-Idan Muka yi nazari akan Wadannan Hadisan zamu fahimci cewa: "Samun jarabawa Daga wajen Mutane ta fuskoki daban-daban sunna ce ilahiyya wadda ba Makawa.

-A kwai lokacin da Imam Zainul abidin (AS) yake cewa wani daga cikin Mabiyansa: Mutane in ka barsu ba za su barka ba, In ka watsar da su ba za su watsar da kai ba, sai Yace wa Imam zainul abidin (AS); ‘to ya zan yi?’ sai ya amsa da cewa: “ka basu daga Mutuncin ka, saboda gobe kiyama”.

Wato Mutum Yayi hakuri daga cutarwar Mutane, Saboda sakamakon da zai samu gobe kiyama.

-Muna Rokon Allah Ta'ala Ya Bamu Sabati.

-Muhammad Jiddah Nguru.
08069306985.

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post