-GA WASU HADISAI DA SUKE YIN HANI GA YIN HASSADA: KU KARANTA KU QARU DAGA AHLIL-BAITY {A.S}

           DAGA TASKAR -Muhammad Jiddah Nguru
                                          08069306985
   -An samo daga Imam Ali (as) Yace, “Mai Hassada Yana bayyanar da sonsa a zantukansa, Yana boye kinsa a ayyukansa, yana da sunan aboki, amma kuma da siffar makiyi.

”Haka nan yazo akan cewa Lukman Yace ma 'Dansa, “Mai HASSADA  Yana da alamomi ukku:

-(1) Yana Yin giba idan Wanda Yake Yiwa HASSADAR Bayanan.

-(2) Yana dadin baki a gaban Wanda Yake Yiwa HASSADA.

-(3) Yana jin dadi idan Musiba ta samu Wanda Yake Yiwa HASSADAR.

-Har Wala Yau a Wani Hadisi da aka samo daga Imam Ali (as) Yace, “Mai HASSADA  Yana farin ciki da sharri (wato idan ya samu wanda yake ma HASSADAR) Yana kuma bakin ciki da murnar Wanda yake yiwa HASSADA.”

-A Wani  Hadisi kuma da aka samo daga Imam Sadik (as) Yace, ”Mai HASSADA bai da jin dadi. ”Wato a zuciyarsa saboda ko wane lokaci  zai kasance cikin damuwa da bakin ciki. kamar yadda yazo daga Imam Ali (AS) yace, “Hassada tana haifar da bakin ciki”.

-Idan Mutum Yayi bincike a littafan Hadisai zai ga akwai hadisai Masu Yawa da suka zo daga Manzon Allah (S) da Ai'mma (AS) da suke sukar HASSADA, ga Wasu daga cikinsu:

-An samo daga Manzon Allah (S) Yace “Kada kuyi kiyayya da ni’imar Allah, aka ce ya Manzon Allah
Wanene zai yi kiyayya da ni’imar Allah? Sai yace masu yin HASSADA. ”

-A wani Hadisi kuma da aka samo daga Imam Ali (AS) Yace: “HASSADA itace mafi sharrin cututtuka wato na zuciya.”

-Har Wala Yau daga Imam Ali (AS) Yace: “Mai HASSADA mai fushi ne ga abun da Allah ta’ala ya hukumta.”

-Haka Nan Wani Hadisi da aka samo daga Imam Sadik (AS) Yace: “Kashedinku sashenku Yayi HASSADA da sashe domin kafirci asalinsa daga HASSADA ne.”

-An Samo daga Manzon Allah (S) Yace, “Kashedin ku da HASSADA, domin HASSADA tana cin ladar kyawawan aikin Mutum kamar yadda wuta ke cin kira-ren itace.”

-A kuma Wani Hadisi da aka samo daga Imam Bakir (as) Yace, “Lalle HASSADA tana cin imani kamar yadda wuta ke
cin kira-ren itace.”

-Haka nan Wani Hadisi da aka samo daga Imam Ali (as) Yace, “Sakamakon HASSADA Shine tabewa duniya da lahira.”

-A Wani Hadisi Kuma Imam Ali (as) Yana cewa: “Ya ishe ka ga mai yin HASSADA Yana bakin ciki lokacin da kake farin ciki.” A wani wajen kuma Yace, “Mahassadi mai Yawan Hasara ne, Maininki baninki na zunubi ne.”

-Saboda haka HASSADA tana da illoli Masu Yawan gaske ga Ma’abucinta, wato ga zunubin da za a rubuta Masa, ga zama cikin bakin ciki, ga rashin Samun ni’imar da yake ma HASSADA, amma ga Wanda Yake ma hassadar ko, shi kuma ga lada da zai samu baya ga ni’imar da yake cikinta, saboda haka daga karshe mai HASSADAR shi Yai Hasara a Duniya da lahira.

-Allah ta'ala ka tsare Zukatanmu daga Wannan Mummunan cuta ta HASSADA.

Barkanku da Safiyar Juma'a

-Muhammad Jiddah Nguru
08069306985.

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post