-GA WATA KISSA MAI DADIN KARANTAWA DAGA IYALAN ANNABI {S}

-An ruwaito daga Jabir 'Dan Abdullahi al-ansary Yace "Wata rana Mun yi Sallar la’asar tare da Manzon Allah (S) bayan Mun idar da sallar Sai Manzon Allah (S) Ya zauna, Sahabbansa Suma suka zauna.
-Sai ga Wani dattijo Yazo
Ya zauna a gaban Manzon Allah (S), Sai Dattijon Yace Ya Annabin Allah, Ni Matafiyi ne Ina jin Yunwa ina bukatar a bani abinci, kuma bani da tufafi ina bukatar a bani tufafi.

-Sai Manzon Allah (S) Yace Masa: "Yanzu ko gashi kazo bani da abunda zan baka, amma duk Wanda Yayi nuni ga Wani aiki na Alkhairi to
Yana da lada kamar Wanda ya aikata,
Saboda haka ka tafi gidan Fatima wadda take son Allah da Manzonsa kuma Allah da Manzonsa suna sonta,

-Sai Manzon Allah Ya cewa Bilal ya tashi ya raka wannan dattijo zuwa gidan Fatima, da suka isa gidan sai dattijon yayi sallama yace, “Assalamu alaikum
ya Ahli baytun nubuwwa”

-Sai Sayyida ta amsa sallamar tace wanene? Sai dattijon yace wani dattijo ne Mabukaci yake neman a taimaka Masa da abinci da kuma tufafi, to kasantuwar a lokacin babu abinci a gidan tun ma kwanaki ukku gabanin haka, sai Sayyida Fatima (as) ta dauki shinfidar da Hassan da Husaini suke kwanciya akai ta dauko ta bashi akan yaje ya sayar domin ya biya bukatarsa,

-Sai dattijjon yace mata a’a ba zai amsa ba, wato yana ganin abun ba zai yi kima ba wajen sayarwa, ganin haka sai Sayyida Fatima (sa) ta shiga gida ta cire abun wuyanta na zinare, a wannan lokacin kamar a ce sarka, sai ta kawo mashi akan yaje ya Sayar da sarkar sai ya siyi abubuwan da yake bukata na abinci da tufafin, sai ko ya amsa, da ya amsa bai tsaya ko ina ba sai wajen Manzon Allah,

-Sai Yace Ya Manzon Allah gashi Fatima ta bani wannan abin wuyan akan in sayar in biya bukatu na da kudin, nan take sai Ammar Dan Yasir ya mike Yace Ya Manzon Allah idan kayi min izini zan sayi wannan Sarkar?

-Sai Manzon Allah (S) Yace na yi maka izini, to sai Ammar ya kebance da Wannan dattijon kan nawa zai sayar masa da abun wuyan? Sai dattijon Yace Masa ka bani abinda zai sai man abinci, in kuma sai tufafi ko da guda daya ne, da kuma dinari ko da daya ne da zan yi guzuri dashi zuwa garinmu, da yake ba Mutumin Madina bane.

-Sai Ammar Ya bashi kayayyakin abinci da tufafi masu yawa da kuma kudi Dinari 20 da kuma dirhami 200, ya kuma bashi dabba ta hawa da zai hau zuwa
garinsu.

-Sai wannan dattijo Ya koma Wajen Manzon Allah (S), sai ya tambaye shin ka samu biyan bukatar ka? Sai Dattijon Yace Ya Manzon Allah na’am na kuma zama Mawadaci yanzu,

-Sai dattijon yai addu’a Yace, “Ya Allah Ta’ala Wanda babu abun bautawa face kai, kabawa Fatima abinda ido bai taba gani ba, kunne bai taba ji ba.”

-Bayan haka sai Ammar Ya dauki Wannan abun Wuya na Sayyida Fatima Yasa Masa turare na almiski bayan haka ya lullube shi a cikin wani kyelle mai kyau, sai ya ba wani daga cikin bayinsa, Yace ya kaiwa Manzon Allah, wato da abun wuyan da shi Wannan bawan duk ya bawa Manzon Allah (S),

-Da Wannan bawa Yaje ya fadi Wannan sako ga Manzon Allah, sai Annabi Yace Masa, ka tafi Wajen Fatima ka bata abun wuyan har da kai a Matsayin bawanta,

-lokacin da bawan Yaje gidan Sayyida Fatima (sa) ya bata abun Wuyan, Sai ta cewa bawan Ya tafi ta ‘Yanta shi.

-An ce lokacin da Manzon Allah (S) yaji haka sai Yace Wannan abun Wuyan mai albarka ne, Ya biya bukatar mai bukata, ya ‘yanta bawa Ya kuma komawa ga Maishi.

-Asalin Sarkar ta Sayyada  Khadija ce Mahaifiyar Sayyada Fatima, bayan tayi Wafati Sai Sayyada Fatima (sa) ta gaji Sarkar, ita kuma ta bawa 'Yarta  Sayyada Zainab (sa).

-A Karbala Sojojin Yazidu suka Kwace Sarkar a Wurin Sayyada Zainab (sa) Amatsayin ganimar Yaki.

-Allahu Akbar 'Yan  akwai Darussa Masu Yawan gaske a cikin Wannan kissa amma ba zan iya fitar dasu ba saboda gudun tsawaita rubutu.

-Allah ta'ala ya Sanya mu a cikin ceton Sayyada Fatima (as), Bihaqqi Sayyid Zakzaky (H).

-Barkanku da Safiyar Talata.

-Muhammad Jiddah Nguru.
08069306985

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post