ME CE CE TASKAR ALLAH MAFI TSADA?

                                                 MASHA ALLAH                             
                                  
Ya zo a Hadisul Kudusi cewa: Annabi Dawud (as) ya yi Munajati da Ubangijinsa yace: Ya Ubangijina!!.. Kowanne Sarki yana da Taska, ya rabbi ina Taskarka take ne!?. Sai Allah Swt ya ce da Shi: "Ina kuwa da Taskar da ta fi Al'arshi girma, ta fi Kursiyyu yalwa, ta fi Aljanna dadi,

Ta fi Malakuti ado, Qasarta ita ce Ma'arifa (Sanin Allah Swt), Samanta shine Imani, Ranarta kuwa shine Shauqi, Watanta shine Son Allah,...Girgijenta kuwa shine Hankali, Ruwan samanta ita ce Rahama, 'Ya'Yan Itatuwanta su ne Da'a, amfanin da za a girba kuwa ita ce Hikima.

Tana da Kofofi hudu: IILIMI, HAKURI, DAURIYA, YARDA DA HUKUNCIN ALLAH, wannan Taskar kuwa ita ce Zuciya".


Littafin Jawahirul Bihar.
.

ISHAQ MUHAMMAD ISHAQ

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post