MU KOYI BOYE SIRRIKAN MU DAGA SHUGABAN MU'MINAI ALI BIN ABU TALIB (AS).

⇀Maytham ya ruwaito: Wani dare  Imam Ali (As) ya bar Kufah ya isa ga Masallacin Jufi. Ya kalli gabas yayi sallah raka'a hudu.
⇀Bayan ya gama sallar ya daga hannuwan sa sama yace; "Ya Allah! Taya zan kiraye ka alhali na kasance mai yawan sabo, da kasa yin biyayya gare ka.

⇀Bayan ya fito daga Masallacin na bishi harsaida muka kai wani hamada, Ali ya zana zana wani layi ya zagaye ni da cewa komi tsanani kada in fita daga iyakar wannan layi.

⇀Ya kasance lokacin ana bakin duhun dare, Imam Ali ya fita shi kadai da sanin yana da makiya masu burin shekar da jinin sa.

⇀Duba da yanayin rashin tsaron shi, yasa ka na bishi duk da nasan hakan rashin biyayya ne ga umurnin sa.

⇀Naga Ali (As) ya dirka kansa da kyau, yana kokarin gana wa da wani. Imam ya fahimci na biyo bayansa.

⇀Ya kallen ya tambaye ni: "Kai waye?". Na Masa mishi da cewa; "Nine Maytham  Imam yace; shin ban gargade ka ba kada ka fito daga zanen dana kewaye ka dashi?.

⇀Na Amsa mishi da cewa; "Ya shugaba na! Tunanin cewa makiya zasu iya farmaka a ko wanni lokaci, ya hana ma zuciya ta samun kwanciyar hankali."

⇀Imam Ali (As) yace; "Amma kataba jin hira ta?" Nace; "A'ah ya shugaba na ban taba jin komi ba". Imam yace; "Ya Maytham! Akwai abubuwa da suke damun zuciya ta, ya kamata in haka rami in bisne sirrika na. Bishiyarda zata toho kuma, zata zam daga irin sirrika na dana ka bisne ne".

Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad....

Don karin bayani a duba, Al-fusul Al-Mi'ah, Mj na 5, Shafi na 409.

           ◉Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ◉

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post