-MUN SAMU DAUKAKA NE DA SOYAYYAR MANZON ALLAH (S) DA AHLUL BAIT (AS).

-Imam Sadik (as) Yana cewa "Duk Wanda Yake Son Ahlul-bait (as) Kuma Ya tabbatar da Soyayyarmu a cikin Zuciyarsa to Babu Shakka Kalaman Hikima Zasu rika gudana akan Harshensa Kuma Imani zai tabbata a cikin Zuciyarsa.
-Wata Rana Imam Ali (as) Ya tambayi Abi Abdullahi Judli cewa 'Shin Kana So in baka labarin Kyakyawan aikin da duk Wanda Yazo da shi Ranar Alkiyama zai amintu daga tsoron Wannan rana, da kuma Mumunan aikin da duk Wanda yaje da shi Lahira Allah zai watsa Masa kayansa a wuta?

Sai Abi Abdullahi Jadly Yace Na'am Ya kai Shugaban Mumunai, Sai Imam Ali  (as) Yace Masa "Kyakyawan aikin Shine Soyayyarmu,  Mummunan aiki Kuma  Shine Yin Kiyayya agare mu.

-A Wani Hadisi kuma Imam bakir (as)  Yana cewa Soyayya agaremu Imani ne, Kiyayya kuma  agaremu Kafirci ne.

-An ruwaito wani Hadisin daga Manzon Allah (S) Yana cewa "Ku lizimci  Soyayyar Ahlul-baiti na Saboda duk Wanda ya hadu da Allah Madaukakin Sarki cikin  Soyayyar Ahlul-bait zai shiga Aljanna da Cetonsu Manzon Allah Yace na rantse da Wanda raina ke hanunsa babu Wani aikin Bawa da zai Masa amfani Matukar bai san hakkinmu ba.

-Daga cikin Wasiyoyin da Imam Ridha (as) Yayi  a cikin littafin Fikhu Ridha (as), Yana cewa "Ku Yawaita Yin Salati ga Manzon Allah (S) tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma kullum ku Yawaita Yin addu'a ga Muminai Maza da Muminai Mata.

-Imam Ya cigaba da cewa "Salati Yana daga cikin fiyayyun aiyuka Wanda Allah Madaukakin Sarki Yayi Umarni da yin shi.

-Imam Yace kuyi Kokarin biyawa Mumunai Bukatunsu, da Sanya farin ciki a cikin zukatansu tare da kore duk wani bacin rai da damuwa da suka shiga, Saboda babu wani aiki da Allah Madaukakin Sarki ya fi so bayan ayyukan farilla kamar Sanya farin ciki a zukatan Mumunai.

-Imam (as) Ya cigaba da cewa "Kada ku bar Aiyuka Managarta tare da kokari a cikin ibadar Allah ta'ala, haka zalika kada ku bar Soyayyar iyalan Gidan Ma'aikin Allah tsarkaka da kuma biyayya a garesu Saboda su abu biyu ne daya baya Wadatarwa sai da 'Dan uwansa guda.

-Ni Muhammad Jiddah Nguru Ina yi Mana  Fatan Allah ta'ala Yasa Mu kara Narkewa a Cikin Soyayyar Manzon Allah (S) da Ahlin Gidansa Tsarkaka.

-Muhammad Jiddah Nguru.
08069306985

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post