SALLAH MAFIFICIYAR IBADA DARASI NA (3) _Kushu'i Cikin Sallah_

 ~Daga Ishaq Mohd Kibiya

   _Bisimillahir Rahamanir Raheem_           
Madaukakin Sarki yana cewa:
‏( ﻗَﺪْ ﺃﻓْﻠَﺢَ ﺍﻟﻤُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻫُﻢْ ﻓِﻲ ﺻَﻼﺗِﻬِﻢْ ﺧَﺎﺷِﻌُﻮﻥَ
Hakika muminai sun rabauta*su ne wadanda cikin sallolin su suke kankan da kai. [1]
ـ ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ 9 :
‏« ﺍﻟﺨﺸﻮﻉ ﺯﻳﻨﺔ ﺍﻟﺼﻼﺓ ‏» .
‏« ﻻ ﺻﻼﺓ ﻟﻤﻦ ﻻ ﻳﺘﺨﺸّﻊ ﻓﻲ ﺻﻼﺗﻪ ‏» .
48-Manzon Allah (s.a.w) ya ce: (kushu'i ado ne ga sallah.
ﻗﺎﻝ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻋﻠﻲّ 7 :
‏« ﻳﺎ ﻛﻤﻴﻞ ، ﻟﻴﺲ ﺍﻟﺸﺄﻥ ﺃﻥ ﺗﺼﻠّﻲ ﻭﺗﺼﻮﻡ ﻭﺗﺘﺼﺪّﻕ ، ﺇﻧّﻤﺎ ﺍﻟﺸﺄﻥ ﺃﻥ ﺗﻜﻮﻥ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓُﻌﻠﺖ ﺑﻘﻠﺐ ﻧﻘﻲ ، ﻭﻋﻤﻞ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺮﺿﻲّ ، ﻭﺧﺸﻮﻉ ﺳﻮﻱّ ‏» .
49-Sarkin muminai Ali (as) ya ce: (ya Kumailu lamarin ba shi ne ka yi sallah ka yi azumi ka bada sadaka ba, kadai dai lamarin shi ne ya kasance sallar anyi ta da tsaftatacciyar zuciya, da kuma aiki wanda yake yarddajje wurin Allah, da tawali'u madaidaici.
ـ ﻭﻟﻤّﺎ ﺳﺌﻞ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻷﻋﻈﻢ 9 ﻋﻦ ﺍﻟﺨﺸﻮﻉ ، ﻗﺎﻝ :
‏« ﺍﻟﺘﻮﺍﺿﻊ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ ، ﻭﺃﻥ ﻳﻘﺒﻞ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﺑﻘﻠﺒﻪ ﻛﻠّﻪ ﻋﻠﻰ ﺭﺑّﻪ ‏» .
50-in da aka tambayi manzon Allah (s.a.w) gameda kushu'i sai ya ce: shi ne yin tawali'u cikin sallah, bawa ya fuskanci ubangijin sa da dukkanin zuciyar sa.
ـ ﻭﺃﻧّﻪ ﺭﺃﻯ ﺭﺟﻼ ﻳﻌﺒﺚ ﺑﻠﺤﻴﺘﻪ ﻓﻲ ﺻﻼﺗﻪ ، ﻗﺎﻝ :
‏« ﺃﻣﺎ ﺇﻧّﻪ ﻟﻮ ﺧﺸﻊ ﻗﻠﺒﻪ ﻟﺨﺸﻌﺖ ﺟﻮﺍﺭﺣﻪ ‏» .
51-lallai shi wata rana ya ga wani mutum yana wasa da gemanyar sa cikin sallah, sai ya ce: (amma lallai shi wannan mutum da ace zuciyar sa ta yi tawali'u da gabban sa ma sunyi tawali'u)
Kushu'i yana kasancewa da zuciya da gabbai tare da juna, annabi (s.a.w) ya kasance idan ya tashi sallah sai fuskar sa tayi jajawur saboda tsananin tsoran Allah madaukaki, Ali (as) ya kasance idan ya tashi sallah ya ce: (na fuskantar da fuskata ga wanda ya halicci sama da kasa) sai kawai ka ga launin sa ya jirkice ya sauya har sai da aka san hakan cikin fuskar sa.
Fadima zahara (as) ta kasance tana tsofaita cikin sallah saboda tsananin tsoran Allah haskenta ya haskaka mala'ikun sama kamar yadda hasken taurari ke haskake halittun da suke kasa, kafadunta sun kasance suna karkarwa cikin sallah ta fuskantar ibadar Allah da dukkanin zuciyarta, haka dukkanin A'imma tsarkaka suka kasance suma kafadun su na girgiza launin fuskar su na sauyawa ya koma ruwan dorawa fatun su su kwansare .
[1] Muminun:1-2


       ~Free Syed Zakzaky Dolee

         ~Daga Ishaq Mohd Kibiya

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post