-TASIRIN KARANTA TARIHIN MANZON ALLAH (S) A ZUKATAN MUMINAI KU SHIGA KUJI

-Muhammad Jiddah Nguru
08069306985
-Wannan Shine Taken Maudu'in da aka bani a Wurin Mauludin Manzon Allah (S) Wanda  Matasan Tijjaniyya (AHABABU RASULULLAHI) Suka Shirya.

-Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin kai, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da Amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S) da Iyalan gidansa tsarkaka (as).

-Da farko zan fara da godiya ta Musamman ga 'Yan Wannan kungiya, Sannan Ina fatan Allah ta'ala ya girmama ladanku, Nagode sosai Allah ya bar zumunci.

-Na so ace Wani Babban Malami kuka bawa Wannan Maudu'i, Saboda Malamai ne kadai zasu  iya yiwa Wannan Maudu'i Adalci. Gashi ni kuma  'Dan Karamin Almajiri ne, Lalle ni ban cancanci tsayawa agaban Malamaina nayi jawabi ba.

-Hakika Karanta tarihin Manzon Allah (S) Yana da Matukar Muhimmanci da fa’ida mai yawa ga dukkan Muminai.

-Ga Kadan daga cikin fa’idojin da ke cikin Karanta tarihin Manzon Allah (S), da farko dai shi kansa Karanta tarihin Annabi Muhammad (S) ibada ce mai girman gaske, Wanda take kusanta bawa da Allah ta'ala cikin gaggawa.

-Sannan yawan Karanta Tarihin Manzon Allah (S) Yana gadar da  ilimi mai Yawan gaske, Sannan Yana karawa Mutum kwadayin neman ilimi.

-Sannan Idan Kana Karanta tarihin Manzon Allah (S) zaka kara fahimtar ilimin Shari’a da Mu'amalat.

-Karanta Tarihin Manzon Allah (S) Yana koyar da Kyawawan 'Dabi’u da halaye na girma da dattaku da karamci da kyauta da yafe laifi da hakuri, da duk wata hanya ta samun rayuwa Mai dadi anan duniya da Lahira.

-Sannan Karanta tarihin Manzon Allah (S) Yana kara fito da hakikanin fassarar ayoyi da Hadisai Masu Yawa, kuma hanya ce ta koyon ibada da Yadda ake neman kusanci da Allah ta'ala.

-Karanta tarihin Manzon Allah (S) Yana karawa Mutum kishin Addininsa, da Jarunta Wajen kare Martabar addini. Sannan Mutum zai  koyi bin tafarki Mafi inganci a addini, zaka koyi Yadda zaka sadaukar da kan ka da dukiyarka don kare Addinin Allah.

-Karanta tarihin Manzon Allah (S) Yana Sanyawa Zuciya Nutsuwa da Kamala da farin ciki, Sannan Yana Maganin Matsaloli Masu Yawa da 'Dan Adam zai iya Shiga a rayuwarsa ta hanyar ganin darussa da abubuwan Misalai Masu kawo Maslaha ga dukan Kalubale.

-Karanta Tarihin Manzon Allah (S) Yana koyar da Jagoranci da iya tafiyar da Mulki da tausaya wa Masu rauni da taitmakon gajiyayyu da yin Mulki na adalci da rikon amana.

-Sannan Karanta tarihin Manzon Allah (S) Yana Dauwamar da Son Manzo Allah (S) a cikin zuciya.

-Da Karanta tarihin Manzon Allah (S) za mu San tsarkakakkiyar Nasabar Annabi (S) da irin rainon da akayi Masa, da yadda ya gudanar da tsarin rayuwarsa mai ban Mamaki da tarin albarka Wanda Allah ta'ala Ya taso dashi a kanta.

-Ta hanyar karanta tarihin  Manzon Allah (S) zamu fahimci Yadda ake cin Nasara a gwagwarmayar addini ko akasin haka,  da kuma nuna juriya da Hakuri akan tafarkin addinin Allah ta'ala.

-Sannan karanta tarihin Manzon Allah (S) Yana kara fito da tarihin Saukar Alkur’ani da Mu’ujizozin Manzon Allah (S) da Sanin falalar Karatun Alkur’ani mai girma.

-Sannan Karanta tarihin Manzon Allah (S) Yana koyar da yadda ake zaman aure da hanyar kyautatawa juna tsakanin Ma’aurata da Yadda ake Soyayya da tausayawa Juna a Zaman aure.

-Karanta tarihin Manzon Allah (S) Yana fito da gagarumin aikin da aka R Wajen Yada wannan Addini na Musulunci tun a farkonsa zuwa Yanzu, da kuma gudunmawar da Muminan Sahabbai Masu daraja suka bayar, da Sadaukarwar da suka yi a farkon Wannan Addinin na Musulunci.

-Karanta tarihin Manzon Allah (S) Yana koyar da Mu Yadda ake fuskantar al’amura Masu Wuya da Sarkakiya idan sun bijiro a tsakanin jama’a, Sannan Zamu koyi Yadda ake cizawa a hura da gano Wuraren rauni da wuraren karfi a cikin Rayuwar al’umma.

-Sannan tarihin Manzon Allah (S) Yana koyar da Yawan ibada da cusa kwadayin bautawa Allah ta'ala dare da rana a zukatan bayi, Sannan karanta tarihin Manzon Allah (S) Yana koyar da Kyautatawa Juna da zaman makwabtaka da Nisantar cutar da juna a Mu’amalolin kasuwanci da zaman Majalisa da yin sulhu a tsakanin Al’umma.

-Bari na takaita Muku
Karanta tarihin Annabi (S) ibada ne.

-Nagode Sosai Allah ya bar zumunci.

Muhammad Jiddah Nguru
08069306985.

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post