AQLAQ:/ -HADISAI DA ZANTUKAN A'IMMA (AS) AKAN MUMINAI.

-Kowanne Mumini Musulmi ne amma ba Kowane Musulmi Yake Mumini ba.” Mumini Shine Wanda Sauran Musulmi suka Kubuta daga harshensa da Kuma hannunsa.”Wato baya cutar da ‘Yan uwansa Musulmi da harshensa misali yi Masu giba ko Annamimanci ko Hassada ko Sharri da dai Sauransu.”

-Kuma shi Mumini ko da Ya fusata to fusatarsa ba zata sa ya yi abinda ya saba ma Shari’a ba.

-Sannan Mumuni ba zai samu hakikanin kamalar imani ba har sai ya siffata da abu ukku:
-Ilimi a fagen addini.
- Tsaka-tsaki a fagen rayuwa.
-Dauriya akan Jarabawowi Na Musibu.”

-Mumini Shine Wanda idan Ya aikata Mummunan aiki Na zunubi, to ya kan yi istigfari.” kuma ya kan Shiga cikin damuwa Matuka akan aikin da ya aikata Na zunubi.

-Shi Mumini baya kwatanta Allah da Halittarsa, Saboda duk Wanda Ya kwatanta Allah Ta’ala da halittarsa to Yayi Shirka, duk kuma Wanda ya Jingina Masa abinda aka hana a jingina Masa to ya Kafirta.

-Shi Mumini kullum zaku ganshi tsaf-tsaf baya zama cikin kazanta Saboda Yana daga cikin Dabi’oin Annabawa yin tsafta da kuma sanya turare.”

-Shi Mumini Kullum Yana tare da Imaninsa, kuma shi Imani Yana da ginshikai guda hudu sune:
-Dogara ga Allah,
-Yadda da hukuncin Allah,
-Sallamawa ga al’amarin Allah,
-Da kuma fawwala al’amura zuwa ga Allah.”

-Sannan Shi Mumini Kullum yana yiwa kansa Hisabi Saboda duk Wanda ya yi ma Kansa hisabi to zai rabauta, Wanda kuma ya gafala da yiwa kansa hisabi to zai yi hasara.

-Shi Mumini Ma'abocin kyauta ne, kullum burinsa Ya bayar da kyauta Saboda Neman Yadar Allah ta'ala, Saboda ita Kyauta itaciya ce a cikin Aljanna rassanta na cikin Duniya, to duk wanda yayi riko da wani reshe daga cikin rassanta to zai shiga Aljanna.

-Sannan Mai yin kyauta Saboda Allah Yana kusa da Allah, Yana kusa da Aljanna, Yana kusa da Mutane, Yana kuma nesa daga wuta.

-Shi Mumini Mutum ne mai yawan Sujuda ga Allah ta'ala, Saboda Lokacin da bawa ya fi kusanci ga Allah Ta’ala shine lokacin da yake cikin sujuda.”

-Allah ta'ala ka Karfafe mu Ka Sanya mu Cikin Muminai.

-Muhammad Jiddah Nguru
08069306985

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post