Hadisai Daga Ahlil-baity {A.s} Masu Dadin Saurara


-Imam Ali (as) Yace: "Salati ga Annabi (s) Yana bice zunubi tamkar Yadda ruwa ke bishe wuta."

(Thawabul A'amal:186)*(1)*
 -Manzon Allah (S) Yace: "Salati gare ni da iyalaina
Yana gusar da Munafunci daga zuciya."

-Akhlak Wal Aadab: 87.

*(2)*
 -Manzon Allah (S) Yana Cewa: Wanda yayi min Salati guda daya, ko kwayar zarra ba za ta rage a zunuban sa ba."

-Bihar: 94.


*(3)*
 -Imam Bakir (as) da Imam Sadik (as) Sunce: "Mafi Nauyin abin da za a dora a Mizanin Mutum ranar Alkiyama Shine Salati ga Manzon Allah Muhammad (S) da iyalan gidansa (as)."

-Bihar: 71.

*(4)*
 -Manzon Allah (S) Yace: "Ranar Alkiyama zan tsaya a Wurin Mizani, duk Wanda Munanan ayyukansa Suka Nauyaya akan kyawawa, zan Kawo Salatin da Yayi Min ina dorawa akan Mizaninsa har sai Kyawawan ayyukansa Sunyi rinjaye dashi".

-Thawabul A'amal: 187.


*(5)*
 -An tambayi Imam Zainul Abidin (S) game da cikar Sallah, Sai Imam Ya amsa da cewa: "Salati ga Annabi da Iyalan Sa tsarkaka (as).


*(6)*
 -Manzon Allah (S) Yace: "Duk inda kuka kasance, to ku Yi Min Salati domin Salatin ku Yana iske ni."


*(7)*
 -Manzon Allah (S) Yace "Duk Wanda Yayi Salati gare ni cikin Littafi, Mala'iku basu gushe ba Suna nema Masa gafara Matuka Sunana Yana Cikin Wannan Littafin

*(8)*
 -Manzon Allah (S) Yace: "Duk Wanda Yayi Mun Salati 1, Allah ta'ala zai yi Masa 10, Wanda kuma Yayi 10, Allah zaiyi Masa 100, Wanda kuwa yayi 100, Allah ta'ala zaiyi Masa 1000, Sannan duk Wanda Yayi 1000, Allah ta'ala ba zai Azabtar dashi da Wuta ba har bada.

*(9)*
 -An rawaito daga Sheikh Suduq Rahimahullah da Isnadi zuwa Imam Muhammad Bakir (as) Cewa An tambaye Imam Menene Mafificin aiki a Ranar Juma'a?

-Sai Imam Bakir (as)  Yace: "BAN SAN WANI AIKI DA YA FI SALATI GA MANZON ALLAH (S) DA ALAYENSA (AS) BA.

-A Wani Hadisin Manzon Allah (S) Yace: "WANDA YA YI SALATI A GARENI RANAR JUMA'A SAU DARI (100) ALLAH ZAI GAFAR TA MASA ZUNUBAN SHEKARA TAMANIN".

-Cikakken Salatin Annabi Muhammad (S) Shine Mafi Soyuwa a Wajen Allah Ta ala.

-Muhammad Jiddah Nguru.

*(10)*
Previous Post Next Post