Amsoshin Tambayoyi Kan Juyayin Ashura Daidai Da Fatawar Ayat. Khamenei (1)

A kwanakin baya ne Cibiyar Kula da Wallafa Ayyukan Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamenei, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, ta sanar da wani shiri na tattaro tambayoyin muminai dangane da Ashura da yunkurin Imam Husaini (a.s) don amsa su daidai da fatawar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei. To bayan tattara wadannan tambayoyin, an mika su wa Hujjatul Islam wal muslimin Muhammad Husain Fallahzadeh, daya daga cikin membobin bangaren amsa tambayoyin fikihu a ofishin Jagoran juyin juya halin Musuluncin.
Ga tambayoyi da amsoshin:
T: Muna son sanin siffofin karbabben juyayin zaman makokin Imam Husaini (a.s) a wajen Ahlulbaiti (a.s)?
Amsa: Yayin amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa juyayi yana da wasu abubuwan lura guda biyu: na farko shi ne abin da (juyayin) ya kumsa da kuma abubuwan da ake fadi a cikinsa. Na biyu kuma shi ne salon da ake gudanar da juyayin. Dangane da abin da ya kumsa, wajibi ne abin da ake fadi ya kasance ba abubuwan da aka haramta ba ne, ba wadanda suka saba wa shari’a ba ne. Wato kada a fadi karya, kada a fadi abubuwan wuce gona da iri (guluwi), kada ya zamanto abin da zai janyo zubar da mutumcin mazhaba, kada ya zamanto abin da zai zubar da mutumci da rage matsayin Imam Husain (a.s) da sauran Ma’asumai (a.s). Haka nan kuma kada ya zamanto abin da zai rage matsayi da mutumcin su kansu muminai masu juyayin. Wato wajibi ne abin da za a fadi ya zamanto akwai tabbas cikinsa, bai saba wa mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ba, bai saba wa matsayin Ahlulbaiti da dai sauran abubuwa makamantan hakan.
Dangane da salon juyayin kuwa; to shi ma dai da farko kar ya zamanto akwai ayyuka na haram a cikinsa. A matsayin misali kida na haram da makamantan hakan. Haka nan kuma kada ya zamanto abin da zai janyo cin mutumcin mazhabar. Wato kada mu yi abin da zai zamanto wani makami a hannun makiya ta yadda za su sami wani abu na yada bakar farfaganda a kan mazhabar Ahlulbaiti da mabiyansu.
A takaice ana iya cewa wadannan su ne siffofin da ya wajaba a ce duk wani juyayi abin karbuwa a wajen Ahlulbaiti (a.s) yana da su.
T: Shin akwai matsala cikin cin abincin da ake rabawa a ranakun Ashura da mutum ba shi da tabbaci kan halascinsa? Ina son amsa ne ta bangaren hukunci na fikihu da kuma bangaren kyawawan halaye. Sannan kuma mene ne hukuncin cin abincin bakancen da mutumin da ba ya fitar da Khumusi ya raba?
Amsa: Dangane da cin abincin da mutum ba shi da yakinin haramcinsa, a matsayin misali wasu suka kawo wa masu juyayi da zaman makoki abinci ko kuma wani mutumin da kuke da yakinin ba ya fitar da Khumusi ya kawo muku abincin bakance, to ra’ayin Jagora a nan shi ne cewa babu matsala cikin cin wannan abincin, don kuwa ba ku da yakinin haramcinsa ko kuma haduwarsa da haram. Wato ba ku da yakinin cewa wannan abincin na haram ne, ba ku da yakinin cewa Khumusi ya hau kansa.
To amma a mahanga ta kyawawan halaye – kamar yadda aka tambaya – wasu suna cewa idan har akwai kudin Khumusi a cikin hakan, lalle yana iya yin mummunan tasiri. Idan har mutum zai iya yin ihtiyadi, lalle yana da kyau. Wato idan dai bai zama dole ba, kada mutum ya ci. Ko kuma ga misali idan har ana shakkun ko Khumusi ya hau kan kudin, to ku da kanku ku fitar da Khumusinsa ko kuma idan ya zamanto kana da shakku kan haramcinsa. A matsayin misali kudi ne da ba a san me shi ba, to sai a cire shi a matsayin mayar da abin da aka kwata ko aka same shi ta hanyar haramun sannan ba a tantance mai shi ba; duk kuwa da cewa hakan ba wajibi ba ne. A hukunci na farko mun fadi cewa babu matsala cikin cin abincin da ba a da yakinin haramcinsa ko kuma haduwarsa da haramun. A mahangar fikihu dai ba haramun ba ne. Amma idan har mutum yana son ya zamanto daga cikin waliyan Allah, to yana da kyau ya nesanci hakan.
T: An yi tambayar cewa mene ne ra’ayin Jagora dangane da gudanar da juyayin Ashura ba tare da riga ba? Idan har ba za a dauki juyayin a bidiyo sannan kuma babu mata a wajen fa? Shin a shar’ance yana ganin hakan a matsayin haramun ne?
Amsa: Yayin amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa Jagora ya kasance yana kiran wasu daga cikin mawakan juyayi da kada su dinga yin juyayin na su tsirara, wato ba riga a jikinsu. To amma hakan ba wai fatawa ce ta fikihu ba da za mu iya cewa haramun ne ba. To idan har babu wadanda ba muharramai ba a wajen, sannan kuma babu munanan abubuwa da ake yi, haka nan makiya ba za su yi mummunan amfani da hakan ba, mai yiyuwa ne mu ce ba haramun ba ne. A matsayin misali ‘yan wasu mutane ne suka taru, sannan kuma ba a dauka a bidiyo, haka nan kuma mazaje ne (ba mata a wajen), don haka sai suka cire rigunansu suna dukan kirjinsu. To amma a takaice kiran da yake yi – a matsayin kira da shawara – shi ne cewa kada mazaje su cire rigunansu yayin juyayin. Saboda me? Don mai yiyuwa ne akwai wadanda ba muharramansu ba a wajen don haka za su gansu, haka nan kuma mai yiyuwa ne makiya su yi amfani da hakan wajen yada bakar farfaganda a kan mazhabar Ahlulbaiti (a.s).
Tambaya: An yi tambayar cewa idan har mutum ya ta bugun fuskarsa a lokacin juyayin Ashura har ya ji wa fuskar rauni, shin akwai matsala cikin hakan?
Amsa: Yayin amsa wannan tambayar yana da kyau a fahimci cewa idan dai har kumburi da yin baki-baki ne, watakila saboda amfani da sarka, sannan kuma babu wata cutarwa ta asali ga jikin mutum, to a ra’ayin Jagora babu matsala cikin hakan. To amma duk wani abu sama da haka wanda mai yiyuwa ne makiya su yi mummunan amfani da shi, a matsayin misali mutum ya raunata kansa da jikinsa kamar masu amfani da wuka wajen saran jiki ko kansu (Tatbir), ko kuma shiga cikin wuta da makamantan hakan da wasu suke yi a wasu wajajen. To ala kulli hal dai wadannan ba wasu abubuwa ne da suke da asali cikin addini ba. Babu wani hadisi da yayi magana kansu sannan kuma tarihin Shi’anci bai ginu bisa hakan ba, kana kuma a halin yanzu makiya suna amfani da irin wadannan abubuwa wajen bakanta mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da mabiyansu. Idan har lamarin ya kai ga haka, to lalle akwai matsala. Amma idan har ya kasance kamar yadda aka saba ne, wato abubuwan da suka kumshi bugun kirji da bugun baya da sarka, mai yiyuwa ne jikin mutum ya yi ja da kuma kumbura, kamar dai yadda aka saba, ba tare da cutar da jiki ba, to hakan babu matsala cikinsa.
T: A wasu wajajen da ake tarurrukan juyayin, saboda yawan jama’a Husainiyoyi su kan cika ta yadda a kan rufe hanyoyin da suke gefe ko kuma hakan ya kan haifar da cinkoso da wahalar tafiya a kan hanyoyi. Shin akwai matsala cikin hakan? Ko kuma masu juyayin su kan daga muryoyinsu, shin akwai matsala cikin hakan idan har hakan ba ya cutar da mutane? Idan har akwai matsala, to ya ya batun halartar irin wadannan tarurruka kuma tare da cewa mutum ya san ba zai samu damar shiga cikin Husainiyar ba?
Amsa: Da farko dai juyayin shahadar Abi Abdillah al-Husain (a.s) yana daga cikin mafiya daukakar hanyoyin kusaci da Ubangiji. Yana da tasiri da albarkoki masu yawan gaske. A saboda haka wajibi ne a kiyaye hakan da kuma raya shi. Rayuwar Jagoran juyin juya halin Musuluncin cike take da misalan hakan ta yadda a wasu ranaku na shekara ya kan shirya irin wadannan tarurruka, inda zai zauna yana sauraren abubuwan da suka sami Imam Husain (a.s) daga bakin malamai. Amma a wasu ranakun, fitowa waje cikin tawaga-tawaga ta masu juyayin, irin su ranar Tasu’a da Ashura, suna daga cikin alamu na addini.
To a dabi’ance a irin wadannan lokuta za a rurrufe wasu hanyoyin, duk da cewa idan da za’a yi wani tsarin da zai sa ba za a rufe hanyoyin ba, shi ya fi. Amma yayin jerin gwanon irin su na Ranar Kudus da ranar 22 Bahman (ranar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran) da irin su Tasu’a da Ashura da makamantansu, a dabi’ance mafi yawan mutane su kan fito. To amma sabanin wadannan tarurruka, a samu wani yanayin da za a rufe hanyoyi, a wata Husainiya ko kuma wani mutum ya shirya taron juyayi a gidansa, ko da kuwa juyayin Shugaban shahidai (Imam Husaini) ne, ya saba wa dokokin gwamnati. Wato lalle akwai matsala cikin rufe hanyoyin mutane saboda taron juyayin da wani mutum ya shirya. Koda yake kamar yadda na ce Tasu’a da Ashura na su hisabin daban ne, don kuwa ana kirga fitowar irin wannan tawagar ta masu juyayi a matsayin wata alama ta addini. Don haka a dabi’ance za a rufe hanyoyi da dama, mutane ma suna da masaniya kan hakan saboda mafi yawa daga cikinsu da su ake yin wadannan tarurrukan. To amma sabanin wadannan tarurruka kan, yana da kyau muminai su kiyaye, kada su rufe wa mutane hanya, kada su daga muryoyin amsa kuwwarsu ta yadda za ta cutar da mutane, haka nan sautin kidan ganguna da sauransu da sauran ayyuka wadanda na gefe ne, irin su sansanoni da ake raba ruwa da shayi da sauransu fisabilillahi. Dukkanin wadannan abubuwa ne masu kyau amma kamata ya yi a yi su a wajajen da ba za su toshe hanyoyin mutane ba, haka nan kuma ba za su takura musu ba. Kamar yadda kuma yana da kyau a kiyaye tsaftar hanyoyin.
Dangane da tambayar da suka yi na cewa shin akwai matsala a halarci irin wadannan tarurrukan? A’a, babu matsala cikin halartar su ko da kuwa babu waje. Sai dai kawai kada a cutar da mutane da rufe musu hanya.
T: Ba da jimawa ba na bude wani shago, sannan kuma bisa la’akari da cewa a watan Muharram a kan sami karin masu sayen kayayyaki a wannan yanki da nake da shagon, sannan kuma ina da bashi a kaina. Don haka na ke son sanin shin akwai matsala idan na bude shagona don saye da sayarwa a ranakun Tasu’a da Ashura?
Amsa: A mafi yawan lokuta dai muminai su kan nesanci wasu ayyuka a ranakun juyayin Ma’asumai (a.s). Ga misali ba sa nishadi, to amma idan suka kulla wata yarjejeniyar ko ciniki babu matsala cikin hakan. A mafi yawan lokuta su kan dakatar da ayyukansu don halartar irin wadannan tarurruka wadanda suna daga cikin alamu na addini. To amma idan har bude shagon naka a wadannan ranaku zai zamanto cin mutumci ga masu juyayin ko kuma ga shi kansa juyayin ko kuma ga Imam Husaini (a.s), to lalle akwai matsala cikin hakan.
To amma idan don dai a bude shagon na wani lokaci ne don biyan bukatun muminai kana daga baya kuma a rufe shi, sannan kuma ba a ganin hakan a matsayin rashin girmamawa ko kuma cin mutumci ga taron juyayi da kuma masu juyayin, ko kuma abin Allah ya kiyaye, ga Imam Husaini (a.s), to babu matsala cikin hakan. A takaice dai kamar yadda muka ce muminai su kan dakatar da ayyukansu a wasu ranaku na musamman irin su Ashura don su halarci taron juyayin shugaban shahidai Imam Husain (a.s).
T: Wasu sun yi tambaya dangane da ra’ayin Jagora kan Tatbir (saran kai da wuka ko takobi yayin juyayi)? Shin wajibi ne mabiya sauran maraja’ai su yi riko da wannan fatawar? Batu na biyu shi ne shin akwai wani bambanci ne da a yi hakan a bayyane da kuma a boye?
Amsa: To ra’ayin Jagora dai kan Tatbir a fili yake. Shi dai yana ganin hakan a matsayin haramun ne. Abin da yake cewa shi ne wannan lamarin dai ba shi da asali – mai yiyuwa ne a shekarun baya a sami wasu suna yi, amma dai cancan tun asali babu irin wadannan ayyukan a tsakanin muminai – bugu da kari kan cewa a halin yanzu makiya suna amfani da hakan wajen yada bakar farfanganda kan mazhabar Ahlulbaiti (a.s).
A yanzu idan kuka shiga wasu shafukan internet, ku ka rubuta kalmar Shi’a, (abin da za ku fara gani shi) shi ne hotunan wadannan masu Tatbir din. A saboda haka a mahangar Jagora wannan aikin haramun ne, wajibi ne kuma a nesance shi. Sama ma da batun fatawa shi ya kasance yana cewa kada ku yi Tatbir har ma yana cewa wannan ba juyayi ba ne, face dai rusa juyayi din ne. A saboda haka ya zama wajibi dukkanin muminai da masu takalidi da sauran maraja’ai - cikin dukkanin girmamawa ga maraja’ai masu girma – su yi riko da wannan umurni, sannan kuma su nesanci irin wadannan ayyuka, wadanda ba juyayi ba ne face dai rusa juyayin. Babu wani bambanci da ya sanya tsakanin yinsa a fili ko a boye. A saboda haka wasu ma sun tambaye shi dangane da cewa shin wasu za su iya tafiya gefe a boye su aikata hakan, sai ya ce bai kamata su yi hakan ba, wato ya hana su yi.
T: Mene ne hukuncin la’antar wasu daga cikin makiyan Ahlulbaiti (a.s) a wajajen taro na jama’a ko kuma a wajaje na musamman?

Amsa: Wadannan suna daga cikin tambayoyin da mai yiyuwa kun sha jin amsarsu kai tsaye ta bakin mai girma Jagora, musamman ma a baya-bayan nan inda ya sha jaddadawa kan hakan. Saboda irin fitinar da ta kunno kai a halin yanzu a duniyar musulmi da kuma irin rikici da zubar da jinin da ke gudana tsakanin wasu musulmin da kuma irin cutarwar da hakan take yi ga duniyar musulmi da kuma amfanuwar da makiya da ma’abota girman kan duniya suke yi daga hakan. A lokuta da dama kun sha jinsa yana fadin cewa ku nesanci cin mutumci ababe masu tsarki na sauran mazhabobi. Ya haramta cin mutumcin ababe masu tsarki na sauran mazhabobi.
Ya kasance mai hana duk wani abin da zai kawo sabani da rarrabuwan kai tsakanin musulmi da kuma ganin hakan a matsayin haramun. A saboda haka wajibi ne muminai su nesanci duk wani aiki da babu amfani a cikinsa, face ma dai zai haifar da sabani tsakanin musulmi da kuma haifar da yaki da zubar da jini tsakanin su ko kuma wulakanta wata mazhaba ko kuma ta wani bangare ya zamanto cin mutumci ne ga sauran mazhabobi. Lalle hakan ba ya halalta.
Tambaya ta biyu da aka gabatar a nan ita ce shin za a iya halartar irin wadannan tarurruka ko kuma a’a. To a nan, a wani lokaci idan ka halarci wannan taron, sannan ka yi wa mai wa’azin ko mai waken da yake fadin irin wadannan maganganu da kiransa da ya nesanci yin hakan, ya kan yarda da nesantar ci gaba da hakan. To a nan ya ma wajaba ka halarci wajen. To amma idan ba haka ba, wato halartarka ba ta da wani tasiri, face ma dai za ta karfafa masu irin wadannan ayyuka na rarraba kan musulmi ne, to lalle ba ya kamata a halarta, a wasu lokuta ma ana iya cewa hakan ba ya halalta. Wajibi ne ma a nesanci hakan.
T: Mene ne ra’ayin Jagora Imam Khamenei dangane da wasu kalmomi da ake amfani da su a wajajen zaman makoki da wakokin juyayin wadanda ba su dace da matsayin wani musulmi kai hatta wani dan’adam ba?
Amsa: A baya, yayin amsa wata tambayar, mun ce wajibi ne a nesanci fadin abubuwan da suke haramun ne – irin su karya ko kuma guluwi dangane da tsarkakan Imamai – haka nan kuma wajibi ne a nesanci fadin abubuwan da suka saba wa matsayi da mutumcin wani mutum musulmi. Musulunci dai yana son mabiyansa su zamanto masu kiyaye mutumcinsu. Ku duba ku gani daga cikin tufafin da Musulunci ya haramta har da tufafin shuhura, wato tufafin da ba su dace da wani mutum musulmi ba. Tufafin da idan mutum ya sa, saboda yanayin launi ko yadda aka dinka shi ko kuma tsarinsa da sauransu, mutane za su dinga nuna mutum da cewa bai dace da shi ba. A saboda haka wajibi ne a nesanci fadin maganganu ko jumloli da ba su dace da matsayin wani mutum musulmi ba ko da kuwa za a fadi hakan ne don nuna kauna ga Ma’asumai ko kuma ga Imam Husain (a.s).
T: A wasu lokuta, ranakun juyayi su kan zo daidai da lokutan farin ciki irin su ranakun Idin Nourouz da sauransu. Mene ne hukuncin raba wa baki alawa da sauran kayayyakin zaki na farin ciki?
Amsa: Kowa dai ya san cewa muminai da masoya Ahlulbaiti (a.s) musamman ma Imam Husain (a.s), su kan yi watsi da abubuwan farin ciki da bukukuwan farin ciki a ranakun juyayinsa. Kai hatta ma tufafin da ke nuna alamu na farin ciki su kan nesance su, haka nan kuma ba sa shirya bukukuwa na farin ciki. Na’am mai yiyuwa ne a daura aure a matsayinsa na sunnar Annabi – to amma dai ba sa shirya bukukuwan farin ciki. Me ya sa? Don girmama Imam Husain da kuma ranakun juyayinsa.
A saboda haka bai dace ba a hada tarurrukan farin ciki da ranakun juyayin Imam Husain ko Annabi (s.a.w.a) ko sauran Imamai (a.s) ba. Bai dace a ce wani mumini yana farin ciki ba. A nan bari in yi muku dan karin bayani: Idan har da gaske muna daukar kanmu a matsayin masu juyayin shahadar Imam Husain ne ko kuma masu juyayin abin da ya sami Annabi ko kuma muna cikin juyayin abin da ya sami sauran Imamai (a.s), to shin ya ya za a yi mutumin da yake cikin juyayin rasa wani abin kaunarsa, wanda ya rasa mahaifinsa ko dansa, zai shirya taron farin cikin? A wasu lokuta wasu mutanen, saboda rasa wani na su, su kan dauki lokaci ba sa shirya tarurrukan farin ciki.

Saboda me? Saboda suna ganin kansu a matsayin wadanda suke cikin yanayin juyayi da zaman makoki ne. To a mahanga ta fikihu dai ba za mu iya cewa haramun ne ba, to amma dai bai kamata ba. Sai dai idan ana ganin shirya irin wadannan tarurruka na farin ciki a wadannan ranaku ko darare a matsayin cin mutumcin wadanda ake juyayinsu a wannan ranar ko kuma cin mutumci ga Annabi da sauran Imamai ko kuma ga Imam Husain, ko kuma shi wanda ya shirya wannan taron, ya shirya shi ne da nufin cin mutumci, Allah ya tsare mu, to lalle hakan haramun ne. Wajibi ne a nesance shi.
T: Sun yi tambayar cewa shin mutum yana iya daga hannayensa sama a lokacin da yake magana da Imamai ko kuma tawassuli da su kamar yadda ake yi yayin addu’a?
Amsa: Kowa dai ya san cewa mu dai Allah kawai mu ke roko; wato neman biyan bukata a wajen Allah ne, muna sanya Imamai ne kawai a matsayin tsanin isa gare Shi. Don haka mu ke tawassuli da su a matsayinsu na Hujjojin Allah. A matsayinsu na waliyan Allah da suke da matsayi na kusaci da Ubangiji, don haka mu ke sanya su a matsayin tsani. Mu ke sanya su a matsayin hanya da tafarkin isa gare Shi Madaukakin Sarki. Wannan dai umurni ne na Alkur’ani.
A saboda haka ne muke sanya su a matsayin tsani da hanyar isa ga Allah Madaukakin Sarki saboda irin matsayin da suke da shi a wajensa. Don haka babu matsala idan mutane suka daga hannayensu sama don yin addu’a – ga misali ga Imam Husain, ga Annabi da sauran waliyan Allah – da neman biyan wata bukata da suke da ita. Babu matsala cikin hakan. Kowa ya san cewa akidarmu ta ginu ne bisa cewa Annabi da sauran tsarkakan Imamai, dukkaninsu bayin Allah ne. Bayin Allah na hakika.
A cikin Tashahhud (tahiya) mu na karanta cewa “Mun shaida cewa babu wani Ubangiji sai Allah, shi kadai ba shi da abokin tarayya”. Shaidawar farko kan kadaitakarsa ne daga nan kuma sai muke cewa “Kuma mun shaida Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa. Wato muna daukar Annabi ne a matsayin bawan Allah sannan kuma manzonsa. Dukkanin manyan maraja’anmu da kuma shi kansa Jagora fatawarsu ta ginu ne bisa cewa a lokacin da wani mutum ya shigo haramin wani Imami, sai ya yi masa sujada, to wannan sujadar haramun ce. Allah ne kawai ake wa sujada.
Babu matsala cikin yin sujadar godiya a matsayin gode wa Allah saboda damar da ya ba shi na samun damar ziyarar. Don kuwa ba wai an yi wa Imamin sujada ba ne. A lokacin da wani ya sumbanci haramin wani imami ko kuma ginin harami, yayi hakan ne saboda tsananin kaunarsa ga mai wannan haramin, ba wai kaunar karfe da duwatsun da aka yi ginin ba ne. Tamkar sumbantar rigar Annabi Yusuf ne da Annabi Ya’akub ya yi da kuma shafa ta a kan idonsa.

T: Me Jagora ya ke nufi dangane da rashin kamatar shigar mata cikin jerin gwanon juyayin (Ashura)? Don Allah ka yi mana bayanin mece ce mahangarsa kan hakan. Don kuwa a ranakun juyayin shahadar Imamai, da dama daga cikin cibiyoyi na addini su kan shirya jerin gwanon juyayi inda suke sanya mata a bayan maza. Shin wannan kasantuwar mata a bayan maza, akwai matsala cikinsa?
Amsa: Da farko dai idan har aka tabbatar da haduwa da cakuduwar maza da mata (a yayin hakan), to haramun ne. Akwai iyakoki na shari’a da aka shata kan hakan. A nan muna kira zuwa ga kiyaye wadannan kan iyakokin na shari’a a wajajen tarurrukan juyayin. Mata su kiyaye hijabinsu a yayin irin wadannan tarurruka na juyayi. Su kiyaye idanuwansu.
Amma dangane da batun cewa mata su shigo cikin sahun jerin gwano na juyayi (ana daga hannaye da bugun kirji da su), to cewa ya ke yi hakan bai dace ba. Bai dace ba mata su shirya tawagar juyayi suna tafiya, kai hatta ma su dinga bin bayan masu juyayin (da irin wannan yanayin). Tun da jimawa ana da tsarin yadda ake ake gudanar da juyayin. Mata suna halartar majalisin juyayi da makoki, amma tare da kiyaye iyakoki na shari’a da kuma hijabi da mutumcinsu.
T: Mafi yawan halkokin da suke shirya tarurrukan juyayi da makoki na unguwanni su kan shafe kwanaki goma suna gudanar da tarurukan juyayin. To su kan janyo wutar lantarkin da suke amfani da ita ne daga turakan wutar lantarki na (gwamnati) da aka kakkafa a kan tituna. Mene ne hukuncin hakan?
Amsa: Idan har suna da izinin yin hakan a hukumance, to babu wata matsala. Idan kuma har da izinin gwamnati suke yi amma da cewa za su biya kudin wutar, to wajibi ne su biya. Amma idan har ba tare da izini suke yi ba, to asalin aikin ya saba sannan kuma dole ne a biya kudin wutar da aka sha. Ala kulli hal wajibi ne masu juyayin Shugaban shahidai su bi dokokin gwamnati da kuma kiyaye baitul mali.
T: Shin akwai karhanci cikin sanya bakin tufafi a ranakun juyayin Shugaban shahidai Imam Husain (a.s)? Bisa la’akari da hukunci na gaba daya da ke cewa akwai karhanci sanya bakin tufafi kana kuma makruhi ne a yi salla da su. To idan har mutum yayi bakance fa, shin bakancen nasa ya inganta.
Amsa:  Akwai wani hukunci na gaba daya da muke da shi dangane da sanya bakin kaya wanda shi ne karhanci sannan kuma yin salla da shi yana rage ladar sallar; wannan kuma ita ce fatawar Jagora din ma. To amma an kebance abaya da rawani da takalmi, ko da a ce bakake ne, babu karhanci cikin su. Har ila yau kuma muna da wani hukuncin na gaba daya dangane da juyayi, wato yana da kyau mutumin da yake cikin yanayin juyayi ya yi abin da ke nuna cewa yana cikin juyayin. Don haka sanya bakin tufafi a yayin juyayin Imam Husain da sauran Imamai, wata alama ce da mai juyayin yake son nuna cewa yana cikin juyayi da makoki ne. A saboda haka babu wannan hukunci na karhanci. A saboda haka idan har wani yayi bakance da sharadin bakance na shari’a, to wajibi ne yayi aiki da wannan bakancen matukar dai zai iya.
To amma yana da kyau a fahimci cewa akwai hanyoyi da salo daban-daban na juyayin. Mai yiyuwa ne ya zamanto ta hanyar sanya bakin tufafi ko kuma ta hanyar nesantar wasu ayyuka na nuna farin ciki ko kuma ta hanyar kuka da sauran hanyoyi na daban. Ala kulli hal muna fatan za a kiyaye irin wannan yanayi na juyayi da ake gudanarwa a halin yanzu.

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post