YANZU-YANZU: Iran ta aike da wasikar gargadi ga kashashen da ke bawa sojojin Amurka mafaka a tekun Farisa


YANZU-YANZU: Iran ta aike da wasikar gargadi ga kashashen da ke bawa sojojin Amurka mafaka a tekun Farisa


Da yake bayyana sakon aikawa da wasikun, Babban kwamandan Sojojin jamhuriyyar Muslunci ta Iran, ya ce an aike wasikun gargadin ne ga dukkan kasashen dake yankin tekun Farisa, kan kiyaye bawa sojojin haramtacciyar kasar Amurka mafaka da makwanci a yankuna da ƙasashen su.


Gagadin ya biyo bayan yawan sintiri da 'yan leken asiri da ake samu a yankuna da kashashen dake yankin tekun na Farisa.


Yace, "Wajibi ne muyi wa wanann zare mugun dauri kamin lamarin ya yi kamari", a cewarsa; Iran tana ganin da fuskantar yawan shawagin jirage Amurka dana Oman a yankin.


"Wannan alama ce na shirin kaiwa Iran hari ko farmakar yaki, don suna farwa ne da leken asiri" Bakiri ya jaddada.

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post