Miliyoyin mutane na ta tudadawa haramin jikan Manzon Allah, Imam Hussain (A.S) don halartar taron arba'in na kisansa a Karbala


Miliyoyin mutane na ta tudadawa haramin jikan Manzon Allah, Imam Hussain (A.S) don halartar taron arba'in na kisansa a Karbala 

Miliyoyin mutane daga sassan duniya daban-daban ne keta rudadawa haramin Sayyid Maulana Imam Hussain yayin da cika kwaki Arba'in da shahadar sa ke qaratowa.

Kamar ko wacce shekara, yadda mutanen duniya 'yan gwagwarmaya da masu kishin 'yan adamtaka, wanda ya hasa Musulmi, kirista Sunni da Shi'a ke halartar wannan babban taro na duniya, bana ma abin sai wanda ya gani da idonsa.

A bana taron ya sami halartar jikoki da 'yayan 'yan gwagwarmayar duniya, wanda ya hada da jikan Nelson Mandela na Afrika da kuma jikan Mahatma Gandi na kasar Indiya.

In ba a manta ba dai, tun bayan É“ullar Korona na ne aka takaita zuwa wanann muhimmin wuri mai albarka, yayin da a bana bayan lafawar annobar aka bude kofa da bawa mutane damar halartar hubbaren jikan Manzon Allah (S.A.W.W).

Bayan gama tattakin Arba'in kuma, ana zuwa wurare da kaburburan bayin Allah dake kwance a kasar ta Iraki, cikin harda kabarin Baqi wanda yawancin iyalan gidan Manzon Allah da Sahabban sa ke kwance a wurin.









0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post