NASIHA TA GA YAN MEDIA DA WAKILCIN HARKA (2)

NASIHA TA GA YAN MEDIA DA WAKILCIN HARKA (2)
-----------
--Karanta ka ga yadda Mallam Zakzaky (H) yayi min intabiyu kan aikin MEDIA.
---------
(Nasir Isa Ali)
-------A shekarar 2007 muka fara wallafa wata mujalla mai suna "WASIYYAH" a Kano. Bayan mun kwashe tsawon lokaci muna wallafa ta,sai maganar kai wa Mallam Zakzaky ziyara ta taso,mun kai wa Mallam Zakzaky (H) ziyara domin neman tabarruki da kuma 'Ijazar cigaba da aikin namu na wallafa ita mujallar ta "WASIYYA" Mun kai ziyarar farko ranar asabar a gidansa dake Gyallesu,bayan gaisawa tare da mika masa kwafin Mujallar har goma sha,sai Mallam yace mana mu dan yi hakuri mu bashi dama yayi nazarin mujallar sosai ala bashi sai mu dawo ranar laraba mu same shi a 'FODIYA ISLAMIC CENTER"
-
Ranar tana yi muka cancara ado muka kama hanyar zuwa Zariya domin ganawa da jagora,inda muka isa Zariya da misalin 12:30 na ranar. Muka shiga muka samu wuri muka harde, tafi: Mu shida muka tafi kamar haka: Mawallafin Mujallar "WASIYYA"
-
Mallam Sunusi Abdulkadir
Mallam Sani Malfa.
Shaheed Muhammad Ali
Mallam Ali Yan awaki
Mall.Jibril Markaz sai
Ni Nasir Isa Ali (Edita)
-
Lokacin da Mallam ya bamu na yi sai ya shigo,Mallam ya sallami kowa har Harisawan dake cikin falon, in banda marigayi Alhaji Danlami (Allah ya jikansa)
Abin da Mallam Zakzaky ya fara tambaya bayan an yi gaisuwa tare da gabatarwa shine 'wanene Editor? sai Mallam Sunusi ya nuna ni (Nasir Isa Ali) sai mallam ya fara yi min tambaya da cewar manene hadafinku? Sai nace masa 'yada ilimin gidan annabta'Sai Mallam ya sake tambayata cewar 'sgphin ko ka taba yin aikin jarida ne? sai na amsa masa da Eh. Wadanne jaridun kayi aiki dasu inji mallam? sai na lissafo wa Mallam jaridu uku da mujalla daya wadanda nayi aiki dasu.
-
Sai ya sake ce min to ko Ka yi karatun addini mai zurfi? Saboda harkar addini (Musamman Mujallar addini ko aikin jarida) sai da ilimi.Sai na bai wa Mallam dan kankanin tarihin karatuna na boko da na addini,Sai ya 'masha Allah (Alamar gamsuwa) sai ya sake tambayata cewar,naga da hausa kuke wallafa mujallar ko? sai nace Eh.
Sai Mallam yace 'na duba rubutun hausar naku babu laifi,to kai a matsayinka na Edita,kana bukatar sanin wasu abubuwa kamar haka.
Misali dole ne ka yawaita karanta litattafan Fiqihu,tarihi Musulunci da na al'ummar musulmi daban daban,da kuma al''adun hausawa saboda duk abinda ka dauko to ka san gurbin da zaka ajiye. Saboda komai da ka gani to yana da muhallinsa,kuma da irin tasirinsa a addini da kuma al'adun wadanda kake yin amfani da harshen nasu. Sannan kuma ka yawaita yin nazarin wasu mujallun wadanda suka dade suna yin shigen wannan aikin da kuka fara,kaga su wasu sun kwashe shekaru suna yi,don haka zaku dada samun Experience'
-
Yayin da Mallam Zakzaky (H) yake yi min intabiyu kan aikin MEDIA su kuma sauran abokan tafiyata sun zura min ido ina ta bada amsa a gaban jagora,amma abinda na lura sosai shine yadda Mallam Zakzaky ya tausasa muryarsa sosai kuma ya matso kusa damu har hannunsa mai albarka suna taba nawa hannun,saboda ya saka mana nutsuwa a ran mu (musamman ni)
-
Sai Mallam yace min,kana bukatar nutsuwa sosai da hakuri,sannan ka saka adalci cikin ayyukan naka da tsoron Allah. Su kuma abokan ayyukan naka (masu rubutu) duk suna da bukatar duk wannan din.
Kuma yakamata ku Sani cewar,ba komai da komai ake bugawa ba,wasu labaran sai kun fara renon tunanin masu karatunku kafin ku sakar musu da wani abin. Musamman Ilimin gidan annabta wanda mafiya yawan mutane basu san shi ba,ko kuma sun jahilce shi. Don haka ku bi komai cikin hikima,basira da ilimi wanna. Ku saka hankali sosai.
-
Na'am na sha intabiyo daga jagora kan aikin media amma har gobe ina alfahri da wannan intabiyu din,domin na san kila bamu da yawa wadanda Mallam Zakzaky da kansa ya yiwa intabiyu kan aikin MEDIA kuma ya sahale musu yin aikin jarida. Daga nan sai mallam Zakzaky yace "Gyaran da zan yi a nan shine: ku daina buga labaran siyasa da na wasanni,duk wadan nan ku bar wa Al-mizan kayanta kar kuyi musu Kutse har a fara samun maganar kishiyanci.Sai Malam ya juya ya kalli Alhaji Danlami, ga dai Alhaji Danlami nan zaune,kuma kun kyaleshi yana jin sirrinku,to a nan ne sai Mallam ya tambayi Alhaji Danlami 'Ko kaima jami'in WASIYYAR ne? (Duk wurin kowa dariya) Sai mallam yace kuma ku mayar da hankalinku wajen yada wasiyyar ahlulbaiti din ga al'u!ma. Yakamata ace munada irin wadannan da daman gaske kuma kowa da inda zai fuskanta,domin isar da wannan sakon,kun ga ai da ayyukan sun yi mana sauki sosai.
Sai Mallam yace min kai kuma Edita Allah ya bada sa'a yayi jagora, zaka iya yin wannan aikin ,don haka aje a cigaba da aikin,kuma banda dai wasa. Sai nayi godiya. ga Mallam.
Wannan ita ce TAZKIYYAR' da na samu daga wajen jagorana abin kaunata game da aikin MEDIA.
-
Daga nan sai Mallam Zakzaky (H) ya juya wajen Shaikh Sunusi Abdulkadir Kano suka ci gaba da maganganu kan yanayin wallafa ita WASIYYA' da kuma sauran al'amura. Mallam ya bai wa Mallam Sunusi wasu shawarwari da kuma 'strategies' har wani wurin muka rika yin dariya sosai sakamakon hirar Mallam Zakzaky da Mallam Sunusi. A karshe Mallam Sunusi yayi wa Mallam Zakzaky arkawarin cewar,zai yi iya iyawarsa wajen saka ido domin baganin babu inda aka kauche daga shawarin jagora. An an ne Mallam. yayi mana addu'a tare da fatan alheei
Bayan mun kammala Ziyarar ne muka fito waje muka dauki Hotuna tare da su Mallam.
Alhamdu lillahi.
-------------------
Nasir Isa Ali.

1/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Post a Comment

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post