MUNASABOBIN WATAN SAFAR. A MAZAHABAR JAFARIYYA SHI'A

ISHAQ MUHAMMAD ISHAQ.
.

23 ga Watan Safar
.

A irin wannan rana ce a Shekara ta 4 bayan hijira, As-Sayyidah Fadimatu bnt Asad bn Haashim bn Abdi Manaaf, Mahaifiyar Imamu Ali (as) ta yi Wafati. Fadimatu bnt Asad (as) ita ce Mahaifiyar Imamu Ali (as), kuma ita ce ta zama Uwa ga Manzon Allah (Saww) bayan da ya rasa Mahaifansa da kuma Kakansa Abdul Muddalib (as).
Sayyida Fadimatu bnt Asad (as) ita kadai ce a duk cikin Mata, Allah Swt yayi wa baiwa ta haihuwar Jaririnta (Imamu Ali as) a cikin Ka'aba mai tsarki. Kuma Allah Swt yayi mata baiwar kasancewa Uwar riko ga Manzon Allah (Saww).

Fadimatu bnt Asad (as) ta kasance Mumina mai cikakken Ikhlasi a cikin Imaninta, kuma ta kasance Mata ga Babban gwarzon kare Manzon Allah (Saww) wato Abu Dalib (as), kuma ta haifi 'Ya'Ya 6 tare da Shi, 'Ya'Yan su ne: Dalib, Aqeel, Ja'afar, Ali (as), Sayyida Ummu Haaniy, Sayyida Jumaanata.  Littafin I'ilaamul warah Shafi na 144.
.

WAFATIN TA AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE TA:
.
An samo daga Abdullahi bn Abbas ya ce: Wata rana Ali bn abi Dalib (as) ya zo wajen Manzon Allah (Saww) yana kuka!, yana fadar: Inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun!. Sai Manzon Allah (Saww) yace da Shi: Ya Ali kame daga kukan. Sai Ali (as) yace: Ya Rasulallah Mahaifiyata Fadima bnt Asad ce ta rasu!. Mai ruwaya yace: Sai Manzon Allah (Saww) yayi kuka!, sannan yace:

"Allah ya jikan Ummarka ya Ali, lallai ta Kasance Uwa a gare ka, kuma ni ma ta kasance Uwa a gare ni. Karbi wannan Rawanin nawa, kuma tafi da wadannan Tufafin nawa, ka yi mata Likkafani da su, kuma ka umarci Matan da za su yi mata wanka, su kyautata wanke ta, kuma kada a fito da ita har sai na zo, al'amarinta yana a hannuna".

Mai ruwaya yace: Sai Manzon Allah (Saww) ya fuskanto bayan sa'a daya, aka fito da Fadima Mahaifiyar Ali, Ma'aiki (Saww) yayi mata Sallah, Sallar da bai yi wa wani irin ta ba, yayi mata Kabbarori arba'in, sannan ya shiga Kabarinta ya kwanta a ciki, ba a ji sautinsa ko Motsinsa ba, sannan yace: Ya Ali shigo, ya Hasan shigo, sai suka shiga Kabarin. Bayan da Ma'aiki (Saww) ya gama abinda yake bukatar yayi a Kabarin, sai yace: Ya Ali, fita, ya Hasan fita, sai duk suka fita daga Kabarin. Sannan Ma'aiki (Saww) ya matsa har ya je daidai inda Kanta yake, sannan yace:

"Ya Fadima, Ni ne Muhammad Shugaban 'Ya'Yan Adam ba ina alfakhari ba ne. Idan Munkar da Nakir suka zo miki suka tambaye ki waye Ubangijinki?  Ki ce Allah shine Ubangijina, Muhammad ne Annabina, Musulunci ne addinina, Alkur'ani ne Littafina, 'Dana (Ali as) shine Imamina kuma Waliyyina. Sannan yace: Allah ka tabbatar wa Fadima da tabbatacen zance.

Sannan Ma'aiki (Saww) ya fito daga Kabarinta, ya zuba Kasa a Kanta, sannan ya buga Hannunsa na dama a kan na Hagu ya kakkabe  kasa a Hannayensa, sannan yace: "Na rantse da wanda ran Muhammad (Saww) yake a ikonsa, lallai Fadima ta ji lokacin da nake buga Hannuna na dama a kan na hagu".

Sai Ammar bn Yasir (R.A) ya mike yace:  Ya rasulallah, Uwata da Ubana su zama fansa a gare ka, ka yi mata Sallah irin Sallar da ba ka yi wa wani Sallah da irin wannan Sallar ba!. Sai Ma'aiki  (Saww) yace:

"Ya Abal Yaqzan, lallai ita ta cancanci ayi mata hakan. Ta kasance tana da 'Ya'Ya da yawa daga Abu Dalib, kuma Alkharinsu ya ksance yana da Yawa, mu kuma namu alkhairin kadan ne, ta kasance tana ciyar da ni, su kuma ba su ci abinci ba, tana tufatar da ni, alhali ba ta tufatar da su ba, tana yi mini kwalliya, alhali ba ta yi musu ba".
.

Sai Ammar yace: To ya Rasulallah, me ya sa ka yi mata Kabbara arba'in?

Ma'aiki (Saww) yace: "Haka ne ya Ammar, na duba ne a Dama na, sai na ga Sahu arba'in na Mala'iku, sai ni kuma na yi mata Kabbara kowanne Sahu Kabbara daya".

Ammar yace: Ya rasulallah, to mun ga ka kwanta a Kabarinta, ba mu ji Sautinka ko Motsinka ba!?.


Sai Ma'aiki (Saww) yace da Shi:

"Hakika dukan Mutane za su tashi tsirara a filin Kiyama, Ni kuma ban gushe ba ina rokon Ubangijina ya tayar da ita a cikin Sutura. Na rantse da Wanda ran Muhammad (Saww) yake a ikonsa, ban fito daga Kabarinta ba har sai da na ga Fitillu biyu na haske a daidai Kanta, da kuma wasu Fitillu biyu na haske a daidai Kafafuwanta, da Mala'ikunta  biyu da aka wakilta suna nema mata Gafara har zuwan tashin Kiyama".

Littafin Biharul anwar Juzu'i na 35 Shafi na 70 Hadisi na 4.
.

Kabarinta na nan cikin Makabartar Baki'a kusa da Kaburburan A'imma (as).
.



ZIYARAR FADIMATU BNT ASAD (AS):


...
"السلام على نبي الله، السلام على رسول الله، السلام على محمّد سيّد المرسلين، السلام على محمّد سيّد الأوّلين، السلام على محمّد سيّد الآخرين، السلام على من بعثه الله رحمة للعالمين، السلام عليك أيّها النبي ورحمة الله وبركاته، السلام على فاطمة بنت أسد الهاشمية، السلام عليك أيّتها الصدّيقة المرضية، السلام عليك أيّتها التقية النقيّة، السلام عليك أيّتها الكريمة الرضية المرضية، السلام عليك يا كافلة محمّد خاتم النبيين، السلام عليك يا والدة سيّد الوصيين، السلام عليك يا من ظهرت شفقتها على رسول الله خاتم النبيين، السلام عليك يا من تربيتها لولي الله الأمين، السلام عليك وعلى روحك وبدنك الطاهر، السلام عليك وعلى ولدك، ورحمة الله وبركاته، أشهد أنّك قد أحسنت الكفالة، وأدّيت الأمانة، واجتهدت في مرضات الله، وبالغت في حفظ رسول الله، عارفة بحقّه، مؤمنة بصدقه، معترفة بنبوّته، مستبصرة بنعمته، كافلة بتربيته، مشفقة على نفسه، واقفة على خدمته، مختارة رضاه، مؤثرة هواه، وأشهد أنّك مضيت على الإيمان، والتمسّك بأشرف الأديان، راضية مرضية، طاهرة زكية، تقية نقية، فرضي الله عنك وأرضاك، وجعل الجنّة منزلك ومأواك، اللهمّ صلّ على محمّد وآل محمّد، وانفعني بزيارتها، وثبّتني على محبّتها، ولا تحرمني شفاعتها، وشفاعة الأئمّة من ذرّيتها، وارزقني مرافقتها، واحشرني معها ومع أولادها الطاهرين، اللهمّ لا تجعله آخر العهد من زيارتي إيّاها، وارزقني العود إليها أبدا، ما أبقيتني، وإذا توفّيتني فاحشرني في زمرتها، وادخلني في شفاعتها، برحمتك يا أرحم الراحمين، اللهمّ بحقّها عندك، ومنزلتها لديك، اغفر لي ولوالدي، ولجميع المؤمنين والمؤمنات، وآتنا في الدنيا حسنة وفي الآخرة حسنة، وقنا برحمتك عذاب النار»
.


Amincin Allah ya tabbata a gare Ki ya Waliyyiya Uwar Waliyyai Fadimatu bnt Asad.
.

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post