-GORON JUMA'A -FALALOLIN KARATUN ALKUR'ANI MAI GIRMA.


-Muhammad Jiddah Nguru.

-Akwai Ruwayoyi Na Hadisai Masu Yawa da aka Ruwaito daga Manzon Allah (S) da Kuma A'imma (as) dangane da falalolin Karatun Alkur’ani, ga Wasu daga Cikin Hadisan Zan Kawo Mana don Na kwadaitar damu Falalar dake Cikin Karatun Alkur'ani Mai Girma.

-Manzon Allah (S) Yace, “Gidan da ake Karatun Alkur’ani a cikinsa Albarkarsa da alkhairinsa Na Yawaita, Mala’iku na halartar gidan, Shaidanu Na Kaurace ma gidan, Kuma Wannan gida zai dunga Haskaka ma Ma’abota Sama Kamar Yadda taurari ke Haskaka ma Ma’abota Kasa. Sannan Gidan da ba a Karanta Alkur’ani a cikinsa albarkarsa  Na Karanta, Mala’iku Suna Kaurace ma gidan, Shaidanu zasu dunga Zuwa gidan.”

-Saboda haka 'Yan uwa Yana da Muhimmanci mu yawaita Karatun Alkur’ani a cikin Gidajenmu da 'Dakunan mu.

-Manzon Allah (S) Yace: “Mafi falalar ibadar al’umma ta Shine Karatun Alkur’ani”. Sai Manzon Allah (S) Yace: “Mafi alhairinku Shine Wanda Ya koyi Alkur’ani kuma ya Sanar dashi”.

-Sannan Manzon Allah (S) Yace: “Zukata suna tsatsa kamar Yadda karfe Yake tsatsa, sai aka ce ya Manzon Allah Menene Yake gusar da Wannan tsatsar? Sai Yace, Karatun Alkur’ani da Kuma tunanin Mutuwa.”

-Imam Sadik (AS) Yace: “Duk Wanda Ya Saurari Harafi daya na Alkur’ani to Allah zai rubuta Masa lada, Kuma za a Kankare Masa zunubi, za kuma a daukaka darajarsa.

-Yan uwa koda ma babu Wannan falalar ai Mutum zai so ranar kiyama kunnensa Ya ba da
Shaida gareshi cewa ya Saurari Alkur’ani dashi.

-Sannan Kuma 'Yan uwa Yana da gayar Muhimmanci Ya Kasance bayan Mutum Ya Karanta Alkur’ani to Ya aikata abun da ya karanta, shine Yasa lokacin da Mutum Yake
Karatun Alkur’ani ana so Ya dun ga lura da kuma tambayar Kansa Umarce-Umarce da Yake Karantawa Na ayoyi ya Umartu dasu? Haka nan Hane-hane da yake Karantawa na ayoyi ya hanu? Domin idan ya Kasance alakar Mutum da Alkur’ani Karantawa ne ba aikatawa, to Wannan zai kasance hujja a Kan Mutum ranar  kiyama.

-Sannan kuma idan Mutum Ya aikata abunda Ya Samu to Yana gadar Masa da ilimin da bai Sani ba kamar dai yadda Yazo a hadisi.

-Shi Alkur'ani zancen Allah ta'ala ne, kuma falalarsa akan sauran Maganganu kamar daukakar Allah ne akan HalittunSa. Sannan Kuma Karanta shi kuwa shi ne abin da Yafi falala Kan dukkan abin da Harshe ke Motsi da shi.

-Manzon Allah (s.a.w.a) Yace: "Duk Wanda ya Karanta Harafi daya daga
cikin littafin Allah, Yana da ladan Wannan Harafi, Kuma shi ladan za a ninka shi sau goma".

-Manzon Allah (S) Yace "Misalin Mutumin da Yake Karatun Alqur'ani alhali Yana Mai Kiyaye shi (hardace shi) to Yana tare da Mala'iku masu girma, da tsarkaka.

-Kuma Misalin Wanda Yake Karanta shi alhalin Yana mai kai- komo da shi "sa'annan Yana Mai tsananin wahala a kansa, to Yana da Sakamako kashi- biyu (sakamakon wahalar da kuma karatun).

Happy Juma'a.

-Muhammad Jiddah Nguru
08069306985

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post