AYYUKAN ALHAMIS TA FARKO A WATAN RAJAB MAI ALFARMA. __ISHAQ MUHAMMAD ISHAQ.

Wannan Alhamis (ta gobe)  ita ce ta farko a wannan Wata na Rajab mai alfarma, kuma ruwayoyi da dama sun zo da ayyukan da ake so a yi a wannan Wunin, da kuma daren juma'a na Ranar, wato Ranar Alhamis din da dare, wanda ya shahara da : "Lailatur-raga'ibi" (Daren kwadayi ga masu bukatu zuwa ga Allah swt)
.

Ga wasu daga cikin ayyukan da ake so a yi a wannan Ranar da kuma Yau da dare:
.

1. Ana so a yi Azumi a wannan Alhamis ta farkon rajab.
.

2. An so a yi Sallah Raka'a 12, Sallama 6 tsakanin magriba da isha, kowacce raka'a fatiha da Inna anzalnahu uku da Kulhuwallahu 12. Idan an kammala sallar sai a ce:
.
"ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADIN NABIYYIL UMMIYYI WA ALA ALIHI"
sau 70.
.
Sai a yi Sajada a ce: "SUBBUHUN QUDDUSUN RABBUL MALA'IKATI WAR-RUH", sau 70. Sannan a dago Kai a ce: "RABBIGFIR WARHAM WATA JAWAZ AN MA TA'ALAMU INNAKA ANTAL ALIYYUL A'AZAM sau 70.
.
Sannan a sake komawa Sajada a ce: SUBBUHUN QUDDUSUN RABBUL MALA'IKATI WAR-RUH sau 70. Sannan a roki bukatun duniya da lahira.
.
Insha'Allahu za a ga ijabah.
.


FALALAR AZUMIN DA KUMA WANNAN SALLAR: Ruwaya ta nuna cewa: Manzon Allah (saww) ya ce:

"Na rantse da wanda rayuwata take a ikonsa, ba wani bawa ko baiwa da za su yi wannan sallar face Allah ya gafarta masa dukan zunubbansa, kuma a ranar farko da aka kai shi kabarinsa Allah zai turo masa da wannan sallar a cikin mafi kyaun sura, a cikin fara'a da harshe mai fasaha!, tana ce masa: Ya kai masoyina ka yi bushara lallai ka tsira daga dukkan tsanani. Sai yace da ita: Kai ne waye? ban taba ganin fuska mai kyau ba irin taka, ban taba shakar kamshi mai dadi ba kamar naka!. Sai tace da shi: Ni ce ladar sallar da ka yi a dare kaza.. a gari kaza... a wata kaza... a shekara ta kaza.. Na zo ne yau in biya ka hakkinka, in debe maka kewa, kuma idan aka taso kiyama zan yi maka inuwa a saman kanka, kuma ba za ka taba rasa gafara ba har abada.
.

3. Ana so a ziyarci Imamu Husain (as) a cikin wannan daren.
.

4. Ana so a karanta Du'au kumail da sauran addu'o'i ma'athurai da ruwayoyi suka nuna ana so a karanta su a daren
.

A fara saka Jagora a addu'a tun farko, sannan sauran Bukatu su biyo baya.
.
Previous Post Next Post