TAKAITACCEN TARIHIN IMAM MUHAMMAD AL-BAQIR(AS):

Nasabarsa: Imam Muhammad Al-baqir(as), d'an Imam Ali Zuinul-Abidin (Assajjad)(as), d'an Imam Husaini Sayyid Shuhada'i(as), d'an Imam Ali(as) da Sayyidah Fatimah(as); 'yar Annabi Muhammad(saw).
Mahaifiyarsa: Fadimah 'yar Imam Hasan(as); yayan Imam Husaini(as); Shugabannin samarin Al-jannah.
Al-kunyarsa: Abu ja'afar(as).
Lakabinsa: Al-bakir (bakirul ulum) (kogin ilimi), Ash-shakir, Al-hadi...
Ranar haihuwarsa: 1 Rajab, shekara ta 57 AH, (a wata riwayar an ce; 3 safar).
Inda aka haife shi: Madina.
Matansa: 1. Ummu farwa; 'yar Al-kasim, 2. Ummu hakim 'yar Asid As-sakafiyya...
'Ya'yansa: 1. Imam Ja'afar As-Sadiq(as), 2. Abdullahi, 3. Ibrahim, 4. Ubaidullahi, 5. Ali, 6. Zainab, 7. Ummu salama.
Tambarin zobensa: Al-izzatu-lillahi.
Tsawon rayuwarsa: shekara 57.
Tsayin imamancinsa: shekara 19.
Sarakunan zamaninsa: Al-walid d'an Abdulmalik, Sulaiman d'an Abdulmalik, Umar d'an Abdulaziz, Yazid d'an Abdulmalik da Hisham d'an Abdulmalik.
Tarihin shahadarsa: 7 Zul-hajj 114 AH.
Inda ya yi shahada: Madina.
Dalilin shahadarsa: Guba da Ibrahim d'an walid d'an yazid; ya ba shi a lokacin halifancin Hisham d'an Abdulmalik.
Inda aka binne shi: Baki'a (Madina).
A ranar 1 ga watan Rajab shekara ta 57 A.H. ne gidan sakon Musulunci ya cika da farin ciki mai girman gaske saboda haihuwar Muhammad bn Ali bn Husain al-Bakir(as), wato Imami na 5 daga cikin Imaman gidan Manzon Allah(saw).
Imam Bakir(as) dai ya rayu sama da shekaru 3 tare da kakansa Imam Husaini(as), don haka ya ga waki'ar nan ta Karbala mai tada hankali. Bayan nan kuma ya ci gaba da rayuwa karkashin kulawar mahaifinsa Imam al-Sajjad(as) duk tsawon lokacin imamancinsa har lokacin da ya yi shahada, a yayin wannan lokaci dai Imam Bakir(as) ya sami ilmuka na Musulunci da kuma gadon Annabawa(as) daga mahaifinsa(as).
Wannan yanayi dai ya sanya Imam Bakir(as) ya kai wani matsayin na ilmi, daukaka, tunani, kwawawan halaye da dai sauransu, da za su ba shi damar jagorantar al'umma gaba daya bayan mahaifinsa(as).
An ruwaito Az-Zubair bn Muslim Al-Makki yana cewa:
"Wata rana mun kasance a wajen Jabir bn Abdullah al-Ansari, daya daga cikin sahabban Annabi(saw), sai ga Ali bn Husain(as) ya iso tare da dansa Muhammadu al-Bakir(as), a lokacin yana dan karami, sai Ali(as) ya ce wa dansa Muhammad(as): 'Sumbanci kan baffanka'. Sai Muhammad(as) ya je ya sumbanci kan Jabir. Sai Jabir, wanda a lokacin ya baya gani; ya tambaya cewa: 'Wanene wannan?’. Sai Imam Ali bin Husain(as) ya ce: “Ai dana ne Muhammad(as)”. Nan take sai Jabir ya rungume shi ya ce: "Ya Muhammad! Kakanka Manzon Allah(saw) yana gaisheka". Sai (wasu da ke gurin) suka ce: kamar yaya; Ya Aba Abdallah?’. Sai ya ce: “Wata rana na kasance a wajen Manzon Allah(saw) a lokacin kuwa Husaini(as) yana zaune a kusa da shi yana wasa da shi, sai ya ce min: ‘Ya Jabir! Za a haifawa dana Husaini(as) d'a da za a kira da sunan Ali, a ranar tashin kiyama za a yi kira cewa shugaban masu ibada ya tashi, a lokacin Ali bin Husain(as) zai mike. Shi ma Ali(as) za a haifa masa da mai suna Muhammad(as). Ya Jabir! Idan ka hadu da shi ka isar da gaisuwata gare shi, ka sani cewar idan har ka ganshi to sauran kwanakin da suka rage maka ba su da yawa".
Haka kuwa ya faru, don bayan kwanaki 3 da wannan ganawa ne; Jabir ya rasu.
Saboda irin dimbin ilmin da yake da shi ne ya sa ake masa lakabi da al-Bakir, wato wanda ya kekketa ilmi, wanda yake bayyana dukkan abubuwan da suka shiga wa al’umma duhu da kuma bayyanar da sirrorin da suke cikin ilmi.
(Al-Irshad na Mufid. Al-Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki....).
Irin matsayin da Imam al-Bakir(as) ya kai ne wajen ilmi da tunani da hangen nesa ya sa al’umma suke taruwa a wajensa don amfanuwa da irin wannan matsayi na ilmi da yake da shi.
Kadan daga cikin abubuwan da gwarzayen Musulunci suka fadi dangane da Imam Baqir(as):
Ibn Al-Imad Al-Hanbali yana cewa: Abu Ja’afar Muhammadu al-Bakir(as) ya kasance daga cikin malaman Madina, ana ce masa Bakir ne saboda keta ilmi da ya yi, wato ya keta shi ya san asalinsa da kuma shiga cikinsa..."
Jabir bin Yazid al-Ja’afi ya kasance idan ya ruwaito hadisi daga gare shi ya kan ce: “Wasiyyin wasiyyai kuma magajin ilmin Annabawa Muhammad bin Ali bin Husain(as) ya ce min..."
(Imam As-Sadik wa Mazahib al-Arba’ , j 2, s 436. Bihar al-Anwar na Majlisi, j 46....).
Imam As-Sadik(as) yana cewa: "Babana (Imam Bakir) ya kasance mai yawan zikiri, ya kasance mai ambaton Allah a lokacin da muke tafiya, haka nan idan muna cin abinci ya kasance mai ambaton Allah, haka kuma tattaunawa da mutane ba ta hana shi ambaton Allah. Na kasance ina ganin harshensa na haduwa da saman bakinsa yana mai fadin La’ilaha illallah, ya kan tara mu ya umarce mu da ambaton Allah har rana ta fito, ya kan umarce wadanda suka iya karatu daga cikinmu da su ta karatu, wadanda kuma ba su iya ba da su ta yin zikiri....".
Imam As-Sadik(as) ya kara da cewa: "Wata rana na je wajen babana a lokacin kuwa yana ba da sadakan dinare 8,000 ga mabukatan garin Madina, kana kuma ya ‘yantar da wasu bayi da suka kai kimanin 11..."
Hasan bin Kathir yana cewa: Wata rana na isar da kuka na akan wata bukata da kuma jafa’in ‘yan’uwa ga Abu Ja’afar Muhammad bin Ali(as) sai ya ce min: "Mummunan dan’uwa, dan’uwan da yake kasancewa tare da kai a lokacin wadata kana kuma ya kaurace maka lokacin rashi". Daga nan sai ya umarci wani bawansa da ya zo da wata jaka da ke dauke da dirhami 700 ya ce: "Ka ciyar da wannan, idan ya kare ka sanar da ni".
Sulaiman bin Karm ya ce: "Abu Ja’afar Muhammad bn Ali(as) ya kasance ya kan saka mana da dirhami 500 zuwa 600 zuwa 1000, kuma ba ya nuna goyon baya ga ‘yan’uwansa ko na kusa da shi (akan saura).
Imam Bakir(as) dai ya kasance yana daukan wadannan nauyi ne ba wai don yana da kudin da ya tara ba ne, face dai shi ya kasance ne kamar yadda dansa Imam Sadiq(as) ya siffanta shi da cewa:
"Babana ya kasance mafi karancin kudi daga Ahlulbaitinsa, amma kuma wanda ya fi su nauyi mai yawa..."
(A'ayan Ash-Shi’a na Muhsin Amin, j 4, s 12....).
Don samun cikakken bayani akan tarihin Imam Al-Baqir(as) zaka iya duba wadannan littafan:
1. Tarikh al-Islam, j 1 (Hisham bin Abdulmalik).
2. Manakib Al Abi Talib, na Ibn Shahr Ashub, j 4, s 191.
3. Dala’il al-Imamah na Tabari, s 104....
Allah ya biya mana da bukatunmu, ya karbi ibadunmu, ya sa Al-Jannah firdausi ce makomarmu; albarkacin Annabi Muhammad(saw) da Ahlul-bayt(as), da darajar watan Rajab!!!

Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com
🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈
Previous Post Next Post