TAKAITACCEN TARIHIN SAYYIDAH FATIMAH AZ-ZAHRA(AS); 'YAR ANNABI MUHAMMAD(SAW), 'YAR SAYYIDAH KHADIJAH(AS), MATAR IMAM ALI(AS), UWAR IMAM HASAN(AS), HUSAIN(AS), SAYYIDAH ZAYYINAB(AS)..., SHUGABAR MATAN TALIKAI KACOKAF, UWAR SHARIFAI ('YA'YA DA JIKOKIN ANNABI(SAW)...:

TAKAITACCEN TARIHIN SAYYIDAH FATIMAH AZ-ZAHRA(AS); 'YAR ANNABI MUHAMMAD(SAW), 'YAR SAYYIDAH KHADIJAH(AS), MATAR IMAM ALI(AS), UWAR IMAM HASAN(AS), HUSAIN(AS), SAYYIDAH ZAYYINAB(AS)..., SHUGABAR MATAN TALIKAI KACOKAF, UWAR SHARIFAI ('YA'YA DA JIKOKIN ANNABI(SAW)...:
MATSIYI, DARAJA DA FALALARTA
Ayoyin Qur'ani da ingantattun hadisai sun ambaci matsiyi, daraja da falalar Sayyidah FatimahAz-Zahra(as) (ma'asumiya) (wacce ba ta taba sabon Allah ba), kadan daga ciki: ayar tsarkakewa (Ayatut-Tat'hir = Q : 33 : 33), ayar Mubahala (Q : 3: 61), Suratul Insan (Dahar) (Q : 76 : 5 - 22), Suratul-Kausar (Q : 108 : 1 - 3)..., Hadisul-kisa'...
TARIHIN HAIHUWAR TA
An haifi Sayyidah Fatimah(as) a garin Makkah, ranar Jumu'a, 20 ga watan Jumadal-Akhir, shekara ta 5; bayan Manzanci, shekara 8; kafin Hijira. Wanda ya yi daidai da 27 Afirilu, Shekara ta 614 Miladiyyah. Wannan shine abinda mafi yawan mabiya Ahlul-bayt(as) su ka fi dauka da inganci.
Akwai wasu riwayoyin masu alamta an haifi Az-Zahra(as) ne a shekara ta 2 bayan wahayi.
Akwai wasu riwayoyi marasa inganci da ke alamta an haifi Az-Zahra(as) ne a shekara ta 5 kafin fara wahayi:
(أخبرنا) أبو إسحاق إبراهيم بن محمد بن يحيى المزكى وأبو الحسين بن يعقوب الحافظ (قالا) ثنا محمد بن إسحاق ابن إبراهيم قال سمعت عبد الله بن محمد بن سليمان بن جعفر الهاشمي يذكر عن أبيه عن جده قال ولدت فاطمة(ر) سنة احدى وأربعين من مولد رسول الله(ص).
- الاستيعاب في معرفة الأصحاب : ابن عبد البر، ج ٤، ص ١٨٩٣. تاريخ الوفاة : ٤٦٣. تحقيق : علي محمد البجاوي. الطبعة : الأولى. تاريخ النشر : ١٤١٢.
- المستدرك : الحاكم النيسابوري، ج ٣، ح ٤٧٦٠، ص ١٦١. تاريخ الوفاة : ٤٠٥. تحقيق : إشراف : يوسف عبد الرحمن المرعشلي. دار المعرفة، بيروت - لبنان.
الكافي: عبد الله بن جعفر وسعد بن عبد الله جميعا، عن إبراهيم بن مهزيار عن أخيه علي بن مهزيار، عن الحسن بن محبوب، عن هشام بن سالم، عن حبيب السجستاني قال: سمعت أبا جعفر(ع) يقول: ولدت فاطمة بنت محمد(ص) بعد مبعث رسول الله(ص) بخمس سنين وتوفيت ولها ثماني عشرة سنة وخمسة وسبعون يوما.
- بحار الأنوار : العلامة المجلسي، ج ٤٣، ص ٩. تاريخ الوفاة : ١١١١. تحقيق : محمد الباقر البهبودي. الطبعة : الثانية المصححة. تاريخ النشر : ١٤٠٣ - ١٩٨٣ م. مؤسسة الوفاء، بيروت لبنان.
MAHAIFIYAR SAYYIDAH FATIMAH AZ-ZAHRA(AS)
Sayyidah Az-Zahra(as) ta ta so cikin kyakkyawar tarbiyyah, wacce babu kamarta. Kasancewar Mahaifiyarta ita ce Sayyidah Khadeejah bintu Khuwailid(as); wacce ta zamto Mafificiya a cikin Matayen zamaninta, harma da na yanzu.
MAHAIFIN SAYYIDAH FATIMAH AZ-ZAHRA(AS)
Mahaifin Az-Zahra(as) shine Shugaban dukkan Annabawa(as) da Manzanni(as), shugaban halitta kacokaf... mafificin halittu; ta wajen kyawun hali da dabi'u.
SIFFAR SAYYIDAH FATIMAHAZ-ZAHRA(AS)
Sayyidah Fatimah(as) fara ce, kyakkyawa, mai kyawun diri. Ta fi kowa daukar kamannin mahaifinta(saw). Ta yi kama da Annabi Muhammad(saw) wajen zamansa, tashinsa, tafiyarsa, maganarsa, murmushinsa(saw)...
DABI'UN SAYYIDAH FATIMAH AZ-ZAHRA(AS)
Sayyidah Fatimah(as) ta taso da kaifin hankali da basira, wacce ta zarce sauran tsararrakinta. Don babu tamkarta a cikin Matayen zamaninta, Ta kasance ta na taimakon mahaifinta wajen isar da sakon Allah, duk da kasancewarta yarinya karama a lokacin, takan nuna fushinta akan abinda kafirai su ke yiwa mahaifinta(saw).
Ta na da kyawu da kwarjini irin na Mahaifinta. Yawan ibadah, ga tsoron Allah. Wannan ya sa ta fi dukkan matayen Halittu a wajen daraja da Mukami.
AUREN SAYYIDAH FATIMAH AZ-ZAHRA(AS)
An daura auren Az-Zahra(as); mai albarka a shekara ta 2 bayan hijira. Bayan yakin Badar. Allah ne ya aiko Mala'ikah Jibreel(as) da sakon cewa; "Allah ya na umartar Annabi(saw) da ya aurar da ita ga Imam Ali(as)".
Ko da ya ke a Riwayar gama-gari, ance Sayyiduna Ali(as) ne da kansa ya nemi aurenta awajen mahaifinta, kuma ya amince ya bashi ita, bayan wasu daga cikin manyan Sahabbai sun nema bai basu ba.
عيون أخبار الرضا(ع): جعفر بن نعيم الشاذاني، عن أحمد بن إدريس، عن ابن هاشم، عن علي بن معبد، عن الحسين بن خالد، عن أبي الحسن علي بن موسى الرضا، عن أبيه، عن آبائه، عن علي(ع) (قال: قال لي رسول الله (ص) يا علي(ع) لقد عاتبني رجال من قريش في أمر فاطمة، وقالوا: خطبناها إليك فمنعتنا وزوجت عليا، فقلت لهم: والله ما أنا منعتكم وزوجته، بل الله منعكم وزوجه، فهبط علي جبرئيل فقال: يا محمد إن الله جل جلاله يقول: لو لم أخلق عليا(ع) لما كان لفاطمة ابنتك كفو على وجه الأرض آدم فمن دونه.
- بحار الأنوار : العلامة المجلسي، ج ٤٣، ص ٩٣. تاريخ الوفاة : ١١١١. تحقيق : محمد الباقر البهبودي. الطبعة : الثانية المصححة. تاريخ النشر : ١٤٠٣ - ١٩٨٣ م. مؤسسة الوفاء، بيروت لبنان.
SADAKIN AUREN SAYYIDAH FATIMAH AZ-ZAHRA(AS)
Sadakin Sayyidah Fatimah(as) kudi ne mai yawan gaske, Imam Ali(as) ne da kansa ya biya sadakin auren Sayyidah Fatimah(saw), ya tanadi sadakin ne ta hanyar sayar da Dir'insa (الدرع).
أمالي الطوسي: جماعة عن أبي غالب أحمد بن محمد الزراري، عن خاله، عن الأشعري عن البرقي، عن ابن أسباط، عن داود، عن يعقوب بن شعيب، عن أبي عبد الله(ع) قال: لما زوج رسول الله(ص) عليا(ع) فاطمة(ع) دخل عليها وهي تبكي فقال لها: ما يبكيك؟ فوالله لو كان في أهل بيتي خير منه زوجتك، وما أنا زوجتك ولكن الله زوجك وأصدق عنك الخمس ما دامت السماوات والأرض. قال علي(ع)؛ قال رسول الله(ص): قم فبع الدرع، فقمت فبعته وأخذت الثمن، ودخلت على رسول الله(ص)، فسكبت الدراهم في حجره، فلم يسألني كم هي ولا أنا أخبرته، ثم قبض قبضة ودعا بلالا فأعطاه فقال: ابتع لفاطمة طيبا...
- بحار الأنوار : العلامة المجلسي، ج ٤٣، ص ٩٤. تاريخ الوفاة : ١١١١. تحقيق : محمد الباقر البهبودي. الطبعة : الثانية المصححة. تاريخ النشر : ١٤٠٣ - ١٩٨٣ م. مؤسسة الوفاء، بيروت لبنان.
YAWAN 'YA'YAN SAYYIDAH FATIMAH AZ-ZAHRA(AS)
Sayyidah Fatimah Az-Zahra(as) ta haifi 'ya'ya 3 kacal, ta yi barin daya. Wadanda ta haifa su ne:
- Imam Hasan(as).
- Imam Husain(as).
- Sayyadah Zainab(as).
- Ta yi barin Al-Muhsin(as), ta dalilin harin da yan ta'adda suka kai a gidanta, wanda hakan ya yi dalilin wafatinta(as).
Malaman Tarihi da Hadisi sun yi Sabani akan cewa ko Sayyadah Fatimah(as) ta na da wata ya mai suna Ummu-Khulthum. Mafi inganci riwaya Ummu-Khulthum ita ce Zainab(r); ita kadai ce 'yar Sayyidah Fatimah(as) mace.
Wasu riwayoyi da ba su inganta ba su na alamta akwai Ummu-Khulthum daban bayan Zainab(as).
SHAHADAR SAYYIDAH FATIMAH AZ-ZAHRA(AS)
Sayyidah Fatimah(as) ta yi shahada a garin Madinah, 3 ko 13 Jumadas-Sani ko Ramadan, Shekara ta 11 bayan Hijira, wata 6 bayan wafatin mahaifinta(saw). Wanda ya yi daidai da 27 ga watan Satumba, shekara ta 632 Miladiyyah. Ta rayu shekaru 18, 28, 27... a Duniya.
كتاب دلائل الإمامة للطبري: عن محمد بن هارون بن موسى التلعكبري عن أبيه، عن محمد بن همام، عن أحمد البرقي، عن أحمد بن محمد بن عيسى، عن عبد الرحمن بن أبي نجران، عن ابن سنان، عن ابن مسكان، عن أبي بصير، عن أبي عبد الله(ع) قال: قبضت فاطمة(ع) في جمادى الآخرة يوم الثلاثاء لثلاث خلون منه سنة إحدى عشر من الهجرة...
- بحار الأنوار : العلامة المجلسي، ج ٤٣، ص ١٦٩. تاريخ الوفاة : ١١١١. تحقيق : محمد الباقر البهبودي. الطبعة : الثانية المصححة. تاريخ النشر : ١٤٠٣ - ١٩٨٣ م. مؤسسة الوفاء، بيروت لبنان.
Allah ya kara girma, aminci da daukaka ga Sayyidah Fatimah Az-Zahra(as); 'yar Annabi Muhammad(saw), matar da ta fi dukkan matayen Halittun Allah kacokaf.
Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com
🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post