TAKAITACCEN TARIHIN IMAM ALI(AS):

Nasabarsa ta bangaren Mahaifinsa: Ali(as) d'an Imran (Abu Talib) (Baffan Annabi Muhammad(saw); Abu Talib da Abdullah uwarsu daya ubansu daya = Abdul-Muttallib).

Nasabar Annabi Muhammad(saw) ita ce nasabar Imam Ali(as); illa iyaka Abdullah ya haifi Annabi(saw), Abu Talib ya haifi Imam Ali(as).

Mahaifiyarsa: Fatima Bintu Asad (Bakuraishiya kuma wacce takula da Annabi Muhammad(saw) lokacin da ya ke karkashin rainon Abu Talib).

Kabilarsa: Quraishawa (Hashimawa).

Lakabinsa: Amirul-munin, Sayyidul-muslimin, Imamul-muttakin, Ka’idul-gurril-muhajjalin, Sayyidul-ausiya, Sayyidul-arab, Al-murtada, Ya’asubuddini, Haidar, Asadullah, Bab Madinatul-Ilm...

Alkunyarsa: Abul Hasan, Abul Hasanain, Abul-Sibtain, Abu Raihanatain, Abu Turab.

Ranar Haihuwarsa: Ranar Juma' a 13 ga Rajab. An haife shi ne a cikin dakin Allah mai alfarma (Ka'abah) a daidai ranar 13 ga watan Rajab shekara ta 23 kafin hijira. 1 October 600 M. (15 September 601 M).

Gurin Haihuwarsa: Cikin Ka'aba Dakin Allah mai al-farma.

Shekarar Haihuwarsa: Shekara talatin bayan Shekarar Giwaye. (Mai gidansa; Annabi Muhammad(saw) ya girmeshi da shekara 30).

Adadin 'ya'yansa: Masana tarihi sun yi sabani kan yawan 'ya'yansa amma suna tsakanin 25 ne zuwa 33 a ruwayoyin daban daban. Wasu na cewa, 'ya'yansa: 36, 18 da cikinsu maza ne 18 kuma mata.

Amma 'ya'yansa da Sayyidah Fatimah Az-Zahra(as) hudu ne = 1. Imam Hasan(as). 2. Imam Husain(as). 3. Sayyidah Zainab(as), da 4. Muhsin (wanda yayi shahada tun kan a haifesa; sakamakon harin ta'addanci da 'yan ta'adda suka kaiwa gidan Az-Zahra(as) bayan shahadar Annabi Muhammad(saw).

Matansa: Fatimah Az-Zahra(as). Umamah bint Zainab, Umm ul-Banin, Laila bint Masoud, Asma bint Umais, Khawlah bint Ja'far, Al-Sahba' bint Rabi'ah.

Hatiminsa: Al-mulku Lillahi Wahidul Kahhar (Mulki na Allah ne Shi kadai mai cikakken rinjaye).

Yakokansa: Ya yi musharaka (tarayya) a yakokin Manzo(saw) kacokaf; banda yakin Tabuka da Manzo(saw) ya umarce shi da ya zauna a Madina domin tafiyar da al’amuranta. Yakokin da ya jagoranta da kansa a lokacin khalifancinsa sune: Al-jamal, Siffaini da An-nahrawan.

Tsawon rayuwarsa: shekara 63.

Farkon Imamancinsa: Safar 28, 11 H. May 28, 632 M.

Tsayin imamancinsa: shekara 30. (656–661 M).

Tarihin shahadarsa: Daren jumma’a 21 ga watan Ramadan 40 H. 31 January 661 M. (29 January 661 M).

Dalilin Shahadarsa: Ibn Muljam (Daya daga cikin Khawarij) ne ya kashe shi; sakamakon harin da ya kai masa yana Sallah, a cikin Masallacin Kufa (Iraq).

Inda aka binne shi: Masallacin garin Najaf madaukaki (Iraq).

Wanda ya gajeshi: Imam Hasan Al-Mujtaba(as).

➖➖➖➖➖➖➖➖

Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com

🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹
Previous Post Next Post