*Waki'ar Ashura (2):* *Daga Abdullahi Isah Wasagu*

*IMAM HASSAN YA ZAMA HALIFAN AL'UMMAH* 

Idan mai karatu na biye da mu a rubutun mu na baya, mun kawo bayani har inda al'umma suka yadda Imam Ali ya jagorance su, wato ya zama Halifan su, bayan wafatin Uthman Bin Affan, wanda daga nan ne somi-somin Waki'ar Karbala sakamakon kiyayyar wasu daga cikin Banu Umayya tun Manzon Allah (SAWW) yana raye. Mun kawo a takaice yadda Imam Ali ya yi yakoka(yaki) da Banu Umayya wanda bayan Shahadar shi wannan kiyayya ta ci gaba a kan 'ya'yansa wato Imam Hassa (AS), Imam Hussaini (AS).


Insha Allahul Azim a rubutu na gaba, za mu warware wata shubuha da mafiya yawan sauran bangarorin mazhabobin Musulunci kamar Malikiyya, Hannafiyya, Hambaliyya, Shafi'iyya suke kokarin hana karanto ita wannan waki'a ta Karbala da kuma abubuwan da suka faru a tsakanin Sahabbai kafin Waki'ar da kuma bayanta. Haka nan, don me yasa Imam Ali, Imam Hassan, Imam Hussaini basu sallama ma Banu Umayya ba ? Shin Imam Alin nan baya daga cikin manyan Sahabban Manzon Allah ne a zamaninin sa ? Koko bama tafakkuri a kan maganganun Mazon Allah ne dangane da 'ya'yan sa Imam Hassan da Imam Hussaini dama dan'uwansa Imam Ali ? Shin wadan nan Sahabbai kuma jinin Mazon Allah za su kasance a bayan bata sakamakon kin mubayi'a ga Banu Ummayya ? 


Babbar abin tambaya a nan ita ce, mai yasa mabiya mazhabar Jafariyya wadanda aka fi sani da Shi'a suke rayawa munasabar waki'ar Karbala ? Me nene darussa da kuma manyan dalilan da suka mabiya Mazhabar Jafariyya Imamiyya suke ke kuka tare da karanto waki'ar Karbala ? Insha Allah, za mu yi bayani a nan gaba.


To, bayan shahadar Imam Ali, al’ummar garin Kufa sun zabi Imam Hassan babban dan Imam Ali kuma yaya ga Imam Husaini a matsayin Halifansu. To  zabe na Halifanci ga Imam Hasan bai yiwa Mu’awiya bin Abu Sufyan dadi a rai ba, dan haka a daidai wannan lokaci tsohuwar bakar gaba da kiyayya ga gidan Imam Ali dama Musulunci ya motsa a zuciyar Banu Umayyah(musamman Mu’awiya). 


Mu’awiya dan Abu Sufyan ya yi amfani da kudi da dukiya wajen kokarin sauya tunani(n) da kwatar Kwamandojin yaki da kuma gwamnonin gundum-gunduma domin su kauracewa Imam Hasan (AS). Imam Hasan don ganin wannan addini ya ci gaba da tafiya da kuma kaucewa farraka na al’ummah, sai ya yarda da yarjejeniyar sulhu da Mu’awiya dan Abu Sufyan.


Imam Hasan ya yi amfani da Iliminsa da kuma zurfin tunani nasa ta yin hukunci da irin yarjejeniyar da Manzon Allah(SAWW) ya yi a Hudaibiyya. Imam ya amince da yarjejeniyar Mu’awiya bisa wadannan matakan:


1- Mu’awiya zai yi jagoranci karkashin Sunnar Ma’aiki da kuma hukunce-hukuncen al-Qur’ani.


2- Mu’awiya ba zai yi nadi ko zabar kowa ba, bayan ya kammala Halifancinsa, wannn zai zama zabe da kuma ra’ayin al’ummar Musulmi.


3- Ba za a yaki mutane ba a duk inda suke, sai dai in sun yi tawaye. Za a tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.


4- Za a daina cin zarafin Sahabban Imam Ali; lafiyarsu, dukiyarsu, iyalansu. Za a tabbatar da walwalarsu da damar ci gaba  da gudanar da harkokin rayuwarsu.


5- Za a daina tsinewa Imam Ali a kan munbarin masallatan juma’a a yayin hudubar juma’ah.


6- Ba za a cutar da Imam Hassan ko dan’uwansa Imam Husaini ba, koda kuwa a asirce ne za a aiwatar da wannan.



Bayan wannan yarjejeniyar, Imam Hassan(AS) ya koma Madina da zama watanni shida bayan rasuwar mahaifinsa Imam Ali(AS).

Wancen yarjejeniya kuma da aka kulla, koda daidai da rana daya, Mu’awiya bai cika alkarwan wannan yarjejeniya ba. Mu’awiya ya yi kunnan uwar shegu da wadannan ka’i’doji na yarjejeniya ta inda ya tara mutanen Kufa yana gaya musu cewa, “Kuna tunanin na amshi mulki ne domin na koya muku Musulunci?, Na amshi mulki ne saboda in mulke ku, kuma duk wanda ya yi yunkurin musu ko tawaye kan haka to yana kan hatsarin rasa ransa".


Mu’awuya dan Abu Sufyan ya share fagen maida Halifanci gado, ta yinkurin nada dansa Yazid a yayin da yake gabda riskar mutuwarsa. Sakamakon bakar kiyayya da Musulunci da kuma iyalan gidan Annabta wanda ya hada da son mulki, Mu’awiya dan Abu Sufyan ya ba matar Imam Hassa Ja’dah ‘yar Ash’ath guba da ta sama Imam Hassan a abinci.


Ya yi alkawarin zai aura mata dansa Yazid. Ja’ada ta aikata wannan mummunar aiki inda ta sama Imam Hassan wannan guba a abinci ya ci, wanda sakamakon kaifin guba ya yi sanadiyyar shahadarsa. Imam Hassan (AS) ya yi shahadah a ranar 28 ga watan Safar yana da shekaru 57 da haihuwa, a shekara ta 50 bayan hijirah.


Bayan shahadar Imam Hassan, mabiyansa dake Iraqi, suka fara shirye-shiryen ganin cewa ya za ai Imam Husaini dan uwan Imam Hassan (AS) ya amshi Halifancin al’ummah ? Wadannan mabiya na Imam Husaini (AS) sun rubuta takarda zuwa ga Imam Husaini don su sanar dashi mubayi’arsu gareshi. Amma Imam Husaini bai amsa ba, a inda ya musu bayanin cewa, “Ba zai saba wancen alkawari na yarjejeniya ba da aka yi tsakanin dan’uwansa Imam Hassan da Mu’awuya dan Abu Sufyan ba, har  lokutan yarjejeniyar sun zo karshe".


Nadi na Yazid ya zama Halifan al’ummah ya bakantama muminai rai ciki  harda Imam Hussaini (AS).


Sauran wadanda basu yarda da zabar Yazid a matsayin Halifa ba sun hada da:


– Abdur Rahman dan Abubakar(Halifa na farko).


– Abdullahi dan Umar(Halifa na biyu).


– Abdullahi dan Zubair( ya yaki Imam Ali a Jamal) da dai sauran manyan mutane a Iraqi da Madina da kuma Kufah.


Zamu ci gaba a rubutu na gaba.

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post