MUHIMMANCIN TAMBAYA A ADDININ MUSULUMCI KU KARANTA KUJI

⇀Da yawan lokuta mutum baisan abuba, amma yana kunyar tambaya sabida kada ace baid ilimi, wanda hakan yana samar da gibi a ibadunsa.
                                                         
⇀Allah baya karbar aiki, sai aikin da akai akan ilimin sanin aiki din, kada mu zauna wawi kamar sauran mutane mu zam masu tambaya da neman sani akan abubuwan  da suka shafi ibada da mu'amalolinmu na yau da kullum.

⇀Mu duba wadannan hadisan muji me Abu Abdallah (As) yake cewa game da tambaya▽

⇀Yazo cikin littafin Al-Kafi, Babi na tara (9) daga Muhammad Ibn Muslim da Burayd Al-Ijli sun ruwaito daga Imam Abu Abdallah (As) yace: "Mutane suna lalacewa ne kadai idan basa tambaya akan abinda basu sani ba."

⇀A wata ruwayar kuma Abdullah Ibn Maymun Al-Qaddah ya ruwaito daga Abu Abdallah (As) cewa, Imam yace; "Wannan ilimin (Ilimin Manzon Allah (S) da iyalan gidansa) yana kulle, mabudinsa shine tambaya." Ali Ibn Ibrahim daga Babanshi,  Nawfal da Sakuni suma duk sun ruwaito irin wannan hadisan daga Abu Abdallah (As).

⇀Yunus Ibn Abdulrahman ya ruwaito daga Abu Jafar Al-Auwal daga Abu Abdallah (As) yace; "Mutane baza su iya komi ba sai sun tambaya, tambaya takan saka mutum ya fahimci hakikanin addini. Ta hanyar tambaya zaku san Imamanku, ku kuma bisu koda zasu fadi wani abu na daban ta hanyar Taiqiyya."

⇀Allah yasa mu dace ya ganar damu abin da bamu sani ba, ya kuma bamu ikon tambayar ababen da muke da bukatun saninsu don cika addininmu.

     ᕙ(⇀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ↼‶)ᕗ

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post