FALALAR WATAN RAJAB DAGA QUR'ANI DA INGANTATTUN HADISAI:

Watan Rajab yana daya daga cikin watanni 4 masu alfarma. Mafi yawan malaman tafsiri sun nakalto cewa; akan wadannan watannin 4 ne; Allah(t) yake cewa:

"ﺇِﻥَّ ﻋِﺪَّﺓَ ﺍﻟﺸُّﻬُﻮﺭِ ﻋِﻨْﺪَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﺛْﻨَﺎ ﻋَﺸَﺮَ ﺷَﻬْﺮًﺍ ﻓِﻲ ﻛِﺘَﺎﺏِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻳَﻮْﻡَ ﺧَﻠَﻖَ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﻣِﻨْﻬَﺎ ﺃَﺭْﺑَﻌَﺔٌ ﺣُﺮُﻡٌ ۚ ﺫَٰﻟِﻚَ ﺍﻟﺪِّﻳﻦُ ﺍﻟْﻘَﻴِّﻢُ ۚ ﻓَﻠَﺎ ﺗَﻈْﻠِﻤُﻮﺍ ﻓِﻴﻬِﻦَّ ﺃَﻧْﻔُﺴَﻜُﻢْ ۚ..." (ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ : 36).

"Adadin watanni a wajen Allah 12 ne, ... daga cikinsu akwai 4 masu alfarma, ...karku zalunci kanku a cikinsu (ta hanyar aikata Sabo... da kin yawaita Ibadah... a cikinsu)..."

Ma'anar ﺃَﺭْﺑَﻌَﺔٌ ﺣُﺮُﻡٌ ۚ su ne: 1. Rajab. 2. Muharam 3. Zul-Qa'ada. 4. Zul-Hajj.

ﺍﻷﺷﻬﺮ ﺍﻟﺤﺮﻡ ﺃﺭﺑﻌﺔ: ﺭﺟﺐ، ﺫﻭ ﺍﻟﻘﻌﺪﺓ، ﺫﻭ ﺍﻟﺤﺠﺔ، ﻣﺤﺮﻡ.

(ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻘﻤﻲ. تفسير الميزان... : التوبة : 36).

Allah(t) ya ambaci wadannan watannin 4 masu alfarma a gurare da dama a Qur'an, kadan daga ciki:

ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ : 5، 36 - 37. ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 217،  194. ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ : 2، 97...

Allah(t) ya hana zaluntar kai a cikin wadannan watannin 4, ta hanyar aikata Sabo... da kin yawaita Ibadah, Addu'o'i, Ayukan alkhairi...

KADAN DAGA CIKIN INGANTATTUN HADISAI AKAN FALALAR WATAN RAJAB

Akwai hadisai masu yawan gaske akan falalar watan Rajab, kadan daga ciki:

An riwaito Annabi Muhammad(saw) yana cewa:

"...Rajab watan Allah ne, watan ne mai girma, an kira shi da ﺍﻷﺻﻢّ saboda ya fi duk sauran watannin alfarma (hurum) da wani matsayi da kebanta dashi, hasalima har a lokacin Jahiliyyah ana girmama watan Rajab, kuma wata ne na Allah(t). Sha'aban watana ne (Annabi)(saw). Ramadan kuma watan Al'ummarta(saw)...":

حدثني محمد بن إسحاق قال حدثنا محمد بن الحسن الرازي قال حدثنا أبو الحسن علي بن محمد بن علي المفتي قال حدثني الحسين بن محمد الوردي عن أبيه عن يحيى بن عباس قال حدثنا علي بن عاصم قال حدثني أبو هارون العبدي عن أبي سعيد الخدري قال: قال رسول الله صلى الله عليه وآله ألا أن رجبا شهر الله الأصم وهو شهر عظيم وإنما سمى الأصم لأنه لا يقاربه شهر من الشهور حرمة وفضلا عند الله وكان أهل الجاهلية يعظمونه في جاهليتها فلما جاء الاسلام لم يزدد إلا تعظيما وفضلا ألا أن رجبا شهر الله وشعبان شهري ورمضان شهر أمتي...

- ثواب الأعمال : الشيخ الصدوق : ص ٥٤ - ٥٨. تحقيق / تقديم : السيد محمد مهدي السيد حسن الخرسان. الطبعة : الثانية. تاريخ النشر : ١٣٦٨ ش.، ﺃﻣﺎﻟﻲ ﺍﻟﺼﺪﻭﻕ ﺹ 319.

An riwaito daga Imam Musa Al-Kazim(as) yana cewa:

"Rajab wata Korama ce a cikin Al-jannah, farinta ya fi nono, dadinta ya fi zuma. Duk wanda ya azumci Rana daya cikin sa, to Allah(t) zai shayar da shi daga wannan koramar":

حدثني محمد بن الحسن قال حدثني الحسن بن الحسين بن عبد العزيز المهتدي عن سيف بن المبارك بن يزيد مولى أبي الحسن موسى عليه السلام عن أبيه المبارك عن أبي الحسن قال: رجب نهر في الجنة أشهد بياضا من اللبن وأحلى من العسل من صام يوما من رجب سقاه الله عز وجل من ذلك النهر.

An riwaito Annabi Muhammad(saw) yana cewa:

"Duk wanda ya azumci Rana daya a watan Rajab, to zai samu yardar Allah(t). Allah zai nisanta shi daga fushinsa, zai a rufe masa kofa daga cikin kofofin wuta".

(ﺛﻮﺍﺏ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ ﺹ 49 ، ﺃﻣﺎﻟﻲ ﺍﻟﺼﺪﻭﻕ ﺹ 319)

Imam Al-Kazim(as) yana ce:

"...ﻣﻦ ﺻﺎﻡ ﻳﻮﻣﺎً ﻣﻦ ﺭﺟﺐ ﺗﺒﺎﻋﺪﺕ ﻋﻨﻪ ﺍﻟﻨّﺎﺭ ﻣﺴﻴﺮ ﺳﻨﺔ، ﻭﻣﻦ ﺻﺎﻡ ﺛﻼﺛﺔ ﺃﻳﺎﻡ ﻭﺟﺒﺖ ﻟﻪ ﺍﻟﺠﻨّﺔ..."

"Wanda ya azumci rana 1 a cikin watan Rajab, to za a nisanta shi daga wuta kimanin tafiyar shekara 1. Wanda ko ya azumci kwana 3, to za a sanya shi a Al-jannah".

(ﺛﻮﺍﺏ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ ﺹ 49 ، ﺃﻣﺎﻟﻲ ﺍﻟﺼﺪﻭﻕ ﺹ 319)

An riwaito, wata rana wani tsoho ya zo wajen Manzon Allah(saw) ya ce masa: Ya Manzon Allah(saw) lalle ba ni da karfin azumtar dukkannin kwanukan Rajab. Sai Manzon Allah(saw) ya ce masa; ka azumci farkon watan, tsakiyarsa da kuma karshensa; to za a ba ka lada kamar wanda ya azumci dukkan watan.

(ﺍﻹﻗﺒﺎﻝ ﺹ 634)

Imam Sadiq(as) yana ce:

"Ranar Al-kiyama mai kira zai yi kira a karkashin Al-arshi, ina Rajabawa (wadanda suka raya watan Rajab)? Sai wadansu mutane su tashi, fuskokinsu suna haske da kuma haskakawa. A kawukansu akwai kambi na mulki, wanda aka yi masa ado da lu'ulu'u da yakuti, kuma kowanne daga cikin wadannan Rajabawa akwai Mala'ika 1,000 a gefensa na dama da kuma 1,000 a gefensa na hagu. Mala'ikun suna ce masa, farin ciki ya tabbata gare ka, ya kai wannan bawan Allah. Sai kira ya zo daga wajen Allah ya ce: "Bayina, na rantse da buwayata! zan girmama makomarku, kuma zan nunnunka sakamakonku. Kun yi azumi saboda ni a cikin watan da na girmama darajarsa." Sai Allah ya ce, "Mala'ikuna ku shigar da bayina Al-jannah."

(ﻗﺮﺏ ﺍﻹﺳﻨﺎﺩ ﺹ 37. ﺍﻟﻌﻴﻮﻥ 2/71).

Idan mutum ya yi binciken riwayoyi na hadisai daban-daban da suka zo dangane da falaloli da darajoji na watannin Rajab, Sha'aban da kuma Ramadan, da kuma shaidar da za su yi wa mutumin da ya girmama su a wannan gida na Duniya; wannan kawai ya isa ya nuna ma mutum cewa lalle wadannan watannin suna da wani Asrar gaibiyya a wajen Allah Ta'ala. Misali wannan Hadisi wanda aka riwaito daga Manzon Allah(saw) ya ce:

"Duk wanda ya san daraja da matsayin watannin Rajab, Sha'aban da kuma watan Ramadan, to wadannan watanni za su yi masa shaida ranar Qiyama cewa ya darajta su da kuma girmama su. Sai mai kira ya yi kira, ya Rajab, ya Sha'aban, ya Ramadan! Yaya wannan bawa ya yi aiki a cikin ku, ya kuma da'arsa take ga Ubangiji? Sai Rajab, Sha'aban da kuma Ramadan, su ce ya Ubangijinmu a cikin mu bai yi wani abu ba face neman yi maka da'a da kuma neman falalarka. Kuma ya yi iya kokarinsa wajen neman yardarka da kuma neman son ka. Sai Allah(t) ya ce ma Mala'ikun da ya wakilta ga wadannan watanni: Me za ku ce dangane da wannan shaida da suka yi ga wannan bawa? Sai su ce ya Ubangijinmu! Rajab da Sha'aban da Ramadan sun yi gaskiya! Wannan bawa ya kasance a wadannan watanni yana mai yin kokari wajen neman yardarka da kuma yi maka da'a. Kuma ya kasance yana mai farin ciki da murna ga wadannan watannin, yana fatan rahamarka da kuma kaunar afuwarka da gafararka…"

Hadisin na da tsawon gaske, ga mai bukatar ganin Hadisin yana iya duba Biharul Anwar juz'i na 94 ko littafin Zadul Ma'ad. Dukkan littafan biyu da aka ambata na Allama Majlisi ne.....

MUNASABOBIN WATAN RAJAB

1 ga watan Rajab: Haihuwar Imam Muhamad al-Bakir(as).

3 ga watan Rajab: Shahadar Imam Ali an-Hadi(as).

10 ga watan Rajab: Haihuwar Imam Muhammad al-Jawad(as).

13 ga watan Rajab: Haihuwar Imam Ali Ibn Abi Talib(as).

15 ga watan Rajab: Shahadar Sayyida Zainab(as).

25 ga watan Rajab: Shahadar Imam Musa al-Kadhim(as).

26 ga watan Rajab: Shahadar Sayyiduna Abu Talib(as).

27 ga watan Rajab; Mab'as (Mi'irajin) Annabi Muhammad(saw).

Munasabobi da ayukan Rajab suna da yawan gaske, mai bukata zai iya kumawa zuwaga Mafatihul-Jinan, Sawabul-a'amal, Zadul-mi'ad, Iqbal-a'amal.....

Allah ya karba mana ibadunmu, ya biya mana bukatunmu, albarkacin Annabi Muhammad(saw) da Ahlul-bayt(as)!!!

➖➖➖➖➖➖➖➖
Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com

🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈

0/Post a Comment/Comments

FADI RA"AYINKA ANAN

Previous Post Next Post