-HADISAI BIYAR DA SUKE HANI AKAN WA HADISAI BIYAR DA SUKE HANI AKAN WASANNI! SANNI!

-(1) Imam Ali (as) Yace: "Ya Ku Mutane! Kuji Tsoron Allah! Ku Sani Cewa Ba a halicci Mutum Kara zube ba, balle Yayi WASA! Kuma ba a bar Mutum Sakaka ba! balle Ya yi Wargi"

-(2) Imam Ali (as) Yace: "Mafi Sharrin abinda ake tozarta Rayuwa a cikinta, Shine WASA (Wargi)"

-(3) Imam Ali (as) Yace: "Lallai Shagaltuwa da Wasa, Yana Janyo fushin Ubangiji, Yana sa Shedan Ya Yarda da Mutum, Kuma Yana Mantar da Alkur'ani."

-(4) Imam Ali (as) Yace: "Majalisin WASA Yana Rusa Imani".

-(5) Manzon Allah (S) Yace: "Dukkan WASA bata ne! Sai a wurare uku: (1) Wajen Tarbiyantar da Dawakan Yaki don su horo da gudu. (2) Wajen Koyan Harbi. (3) Sai kuma WASAN Miji da Matar sa.

-ME AKE NUFI DA WASA?

-Wasa Shine Shagaltuwar Mutum da abinda ba zai amfana da shi anan duniya da lahira ba.

-Sannan ita Shagaltuwa da Wasanni a rayuwa Yana daga cikin 'Dabi'a da halaye Na Wawaye da Kafirai, Wanda suka Manta da Manufar zuwansu duniya ko Kuma Suka bijire wa Manufar da aka halicce su dan ita!.

-Don haka shi Wawa Kullum Yana tozarta lokacinsa ne Wajen WASA DA WARGI!

-Kuma Shi Wawa Kullum bashi da aiki sai zaman Jangwam, da zuwa Dandalin Hira, ko zuwa Wajan Kallon WASA ko Fina finai ko Shagaltuwa da "Social Media" a wannan zamani ba tare da tsara lokacin sa ba, ko yin amfani da abinda zai amfanar dashi duniya da lahira.

-Shi Wawa Mai WASA da rayuwarsa a kowanne lokaci Yana tozarta rayuwarsa ne da Wasanni, Kuma Ya Manta da Allah, Baya Zikiri, Baya tunanin Lahira, don haka za kaga Yana WASA da Sallah Kuma baya tashin dare Yayi Nafila, Babu Azumin Nafila! Babu karatun Alkur'ani mai girma, kuma babu Ai'kin Alheri, sai shiga safgar da ba ruwansa, da shiga hakkin Mutane na kusa dana Nesa!.

-YA KAI 'DAN UWA MAI GIRMA KAR KA YI WASA DA RAYUWARKA! KAR KA YI WASA DA LOKACINKA! KAR KA YI WASA DA LAFIYARKA KAR KA YI WASA DA NI'IMAR DA ALLAH YA BAKA! KAR KA YI WASA DA FURSA DA ALLAH YA BAKA! KAR KA YI WASA DA KURUCIYRKA! KAR KA YI WASA DA TSUFANKA!

-SABODA RAYUWA NI'IMA CE  DA ALLAH TA'ALA YA BAKA DON KA KYAUTATA AMFANI DA ITA BA DON KAYI WASA KO KA TOZARTA TA BA.

-FURSA ITAMA NI'IMA CE DA BAIWA DA ALLAH YA BAKA DON A GWADA KA KO ZAKA KYAUTATA AMFANI DA ITA.

-KUMA KA SANI CEWA AMANA CE ALLAH YA BAKA. LALLAI KASAN DA CEWA MUTUWA DA RAYUWA DUKKANSU JARRABAWACE, DUNIYA KUMA ITACE GIDAN JARRABAWAR, WASU ZASU CI WANNAN JARRABAWAR WASU KUMA ZASU FADI, GWARGWADON YADDA KOWANNEN MU YA KYAUTATA AMFANI A RAYUWARSA DA LOKACIN SA DA KUMA NI'IMOMIN DA ALLAH YAYI MASA A DUNIYA, GWARGWADON IRIN NASARAR DA KOWANNEN MU ZAI SAMU A LAHIRA.

-ALLAH YASA MU DACE!

-MUHAMMAD JIDDAH NGURU
08069306985
Previous Post Next Post